Gwamna Abba Ya Ji Koken Jama'a, Ya Tuna da Fursunoni a Kano, Ya ba Su Tallafi

Gwamna Abba Ya Ji Koken Jama'a, Ya Tuna da Fursunoni a Kano, Ya ba Su Tallafi

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ɗauki ga fursunonin da ke tsare a wasu daga cikin gidajen gyaran hali a jihar
  • Abba Yusuf ya ba da gudunmawar abinci da sauran kayayyaki more rayuwa ga fursunonin a gidajen gyaran hali guda uku
  • Hakazalika gwamnan zai ɓullo da tsarin biyan basussukan da aka biyo fursunoni waɗanda ba su fi Naira miliyan ɗaya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da gudunmawar abinci da kayayyakin more rayuwa ga fursunoni a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da gudunmawar kayayyakin ne ga fursunonin da ke manyan cibiyoyin gyaran hali guda uku a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya ba fursunoni kayan abinci Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta ce cibiyoyin da suka amfana da wannan tallafi sun haɗa da Kurmawa da Janguza da kuma cibiyar gyaran Hali ta Goron-Dutse.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya kyautatawa fursunoni

Yayin da aka gabatar da tallafin a hukumance a Kurmawa, Gwamna Abba, wanda kwamishinan harkokin jin ƙai da rage Talauci, Hon. Adamu Aliyu Kibiya ya wakilta, ya ce an ba da tallafin ne domin kyautata rayuwa da walwalar fursunoni.

“Wannan tallafi na cikin ƙoƙarin da gwamnatinmu ke yi don tallafawa rayuwar fursunoni da kuma taimaka musu wajen sake tsayuwa da ƙafafunsu."
"Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi amanna da ba wa kowanne ɗan ƙasa, har da waɗanda ke tsare, damar gyara rayuwarsu."

- Hon. Adamu Aliyu Kibiya

Kayayyakin da aka ba fursunoni

Tallafin ya ƙunshi shanu biyar, buhu 300 na shinkafa (25kg), katifa 4000, matashin kai 4000, bargo 4300, ruwan leda 1500, katon 750 na lemun sha, jarka 60 na man girki (mai girman lita 25L)

Sauran kayayyakin sun haɗa da, katon 25 na maggi, katon 90 na biskit da alewa, katon uku na madarar jarirai, katon 20 na sabulun wanka da katon 15 na kayan tsaftar mata.

Gwamna Abba zai biya basussukan fursunoni

Gwamna Abba Kabir ya kuma sanar da shirin biyan basussukan fursunonin da ke tsare saboda basussuka ƙanana.

“An kafa kwamitin da zai tattara sunayen fursunonin da ke da bashin da bai wuce Naira miliyan ɗaya ba. Gwamnati za ta biya waɗannan basussuka a wani bangare na shirin maido da su cikin al’umma."

- Hon Adamu Aliyu Kibiya

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba zai biyawa fursunoni basussuka Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A nasa jawabin, shugaban gidan gyaran hali na Kurmawa, DCCS Ibrahim Rambo, ya yaba da irin tallafin da gwamnati ke ci gaba da bayarwa.

“Mun gode ƙwarai da wannan babbar gudunmawa. Za mu tabbatar an yi amfani da ita yadda ya dace, cikin gaskiya da adalci."

- DCCS Ibrahim Rambo

Gwamna Abba zai ɗauki masu tsaron makarantu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin ɗaukar masu tsaron makarantu.

Gwamna Abba ya ba da umarnin ɗaukar masu tsaron makarantun ne har mutum 17,600 inda za a kai 400 kowace ƙaramar hukuma domin samar da tsaro a makarantu.

Ma'aikatan za a ba su horon da ya dace kafin a tura su zuwa makarantu, za su yi aiki ta hanyar yin haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng