Yaki da ta'addanci a Najeriya
Miyagun yan bindiga sun halaka wani malamin makaranta da mutane biyu da shugaban matasa a kauyen Tudun Mare da Gefe a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna.
A wani sakon murya da ake yaɗawa, wani kwamandan mayakan ESN a yankin kudu maso gabashin Najeriya ya yi wa gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, barazana.
Gwamnatin Najeriya ta sake yin karar Mazi Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar masu neman kafa Biyafara, wato IPOB, kan wasu sabbin tuhume-tuhume 7.
Yan bindiga da suka yi garkuwa da kananan yara 20 daga garin Kusherki a karamar hukumar Rafi jihar Neja sun bukaci a biya su Naira miliyan 40 matsayin fansa.
Rabi'u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023 yace zai yi sulhu da kungiyar IPOB da sauran kungiyoyin yan bindiga idan ya zama shugaban kasa.
Kasar Birtaniya ta sake sabbunta rahoton shawarwari na tafiye-tafiye da ta fitar inda ya yanzu da lissafa wasu jihohin Najeriya 12 da akwai barazanar hari.
‘Yan bindiga sun sake garkuwa da mutane, hakan na zuwa ne kwanaki bayan dauke wasu gona. Har yanzu ana fama da matsalar kashe-kashe da satar mutane a Zamfara.
Manyan ‘yan majalisar Shura na kungiyar ISWAP,Ali Kwaya da Bukar Mainoka tare da wasu ‘yan ta’addan sun mutu sakamakon bama-bamai da sojin sama suka Harba musu.
Rahotanni da suka shigo sun bayyana cewa yara da yan ta'adda suka sace a garin Mairuwa a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a gona sun shaki iskar yanci.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari