'Ba Makaranta ba ce,' An Samu Sababbin Bayanai kan Harin Boko Haram a Borno

'Ba Makaranta ba ce,' An Samu Sababbin Bayanai kan Harin Boko Haram a Borno

  • Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Kautikari da ke Chibok a jihar Borno ranar Asabar da yamma
  • Maharan sun kashe mutum guda tare da kona ajujuwa biyar da ofishin malamai a makarantar sakandaren gwamnati da ke yankin
  • Sai dai wani masanin tsaro ya karyata cewa an kai hari wannan makaranta duk da bayanin da aka samu daga 'yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari makarantar sakandaren gwamnati da ke ƙauyen Kautikari a ƙaramar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun ƙona wani gini da ke ɗauke da ajujuwa biyar tare da ofishin ma’aikata a makarantar.

Ana zargin 'yan ta'adda sun farmaki wata makaranta a chibok, jihar Borno.
Taswirar jihar Borno da ke a Arewa maso Gabashin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan ta'adda sun kai hari Chibok

An ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:45 na yammacin ranar Asabar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi

Sakataren ilimi na ƙaramar hukumar Chibok, Malah Kyari, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Malah Kyari, wanda ya yi magana da 'yan jarida ya bayyana cewa ɓangaren ƙaramar sakandare na makarantar ne ya fi fuskantar barna a harin

“'Yan ta'addar sun kai hari ƙauyen Kautikari jiya, sun kashe mutum guda sannan suka banka wa wani sashe na makarantar JSS wuta,” in ji Malah Kyari.

‘Yan sanda sun yi magana kan harin

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, shi ma ya tabbatar da harin.

Channels TV ta ruwaito ASP NAhum Daso ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar dakile harin bayan musayar wuta da maharan.

A cewarsa, bayanan da suka samu daga jami’in ‘yan sanda na yankin Chibok sun nuna cewa maharan sun kashe wani mutum mai shekara 50 kafin daga bisani jami’an tsaro su kore su daga yankin.

“Maharan sun samu damar kashe mutum guda sannan suka ƙona wasu gine-ginen ajujuwa kafin jami’an tsaro su fatattake su,” in ji Daso.

Kara karanta wannan

Yadda yakin Iran da Isra'ila, Amurka ya jawo matsala ga tsaron Najeriya

Wani jami’in kula da harkokin ƙananan hukumomi da masarautu a yankin Bama, Chibok, Gwoza, Askira/Uba da Damboa, Samaila Manza, ya ce har yanzu suna tattara cikakken bayani kan barnar da aka yi.

'Ba makaranta aka farmaka ba' - Zagazola

Sai dai, masanin tsaro, Zagazola Makama ya karyata cewa an farmaki makarantar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce 'yan ta'addar sun farmaki jami'an 'yan sa-kai ne, ba wai dalibai ba.

"Wannan wuri ya zama sansanin mafarauta, ba wai ana amfani da shi a matsayin makaranta ba, kuma babu dalibai a wurin a lokacin da aka ce an kai harin.
"Mafarauta ne suka mayar da makarantar sansaninsu don sa ido kan tsaron yankin, da kuma bada gudunmawa ga dakarun Operation Hadin Kai. 'Yan ta'addar sun farmaki mafarautan ne ba wai makarantar da ke dauke da dalibai ba."

- Zagazola Makama.

Karanta bayaninsa a kasa:

MDD ta yi magana kan sace dalibai

A wani labari, mun ruwaito cewa, Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ta fara ruguza aminci da tsaron da ake da shi a makarantu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Makonni da sace dalibai a Borno, Boko Haram ta babbake makarantu a Chibok

Ta bukaci hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya da su gaggauta yin duk mai yiwuwa wajen kubutar da daliban Oyo da Borno.

Wannan na zuwa ne bayan wasu 'yan ta'adda sun shiga makarantu daban-daban a jihohin Oyo da Borno, inda suka sace dalibai da malamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com