‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari

‘Yan Bindiga Sun Hargitsa Kauye, Sun Yi Awon Gaba da Basarake da Mutanen Gari

  • Miyagun ‘yan bindiga sun kuma aukawa wani kauye a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara
  • Ana maganar an yi awon gaba da Mai garin Kwangami, har zuwa yanzu ba a sake jin labarinsa ba
  • Baya ga haka, ‘yan ta’addan sun dauke mutum 6 yayin da Bayin Allah da-dama ke jinyar raunuka

Zamfara - Rahoto ya zo cewa ‘yan ta’adda sun shiga karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, sun kuma ci karensu babu babbaka.

Jaridar Punch tace wadannan mutane masu tada kayar baya sun yi nasarar dauke Mai garin wani kauye, Kwangami a jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin Zurmi mai suna Dahiru Amadu ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun shigo masu dauke da manyan makamai.

A ranar Litinin dinnan ne miyagun ‘yan bindigan suka dauke har da Mai garin Kwangami, Mai martaba Muhammad Galadima.

Kara karanta wannan

NDLEA: Yadda muka yi ram da makaho ‘Dan kasar waje dauke da miyagun kwayoyi

An hada da mutane 6

Baya ga Alhaji Muhammad Galadima, an dauke wasu mutane shida da ake zargin an yi garkuwa da su ne domin a karbi kudin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Dahiru Amadu ya fada da ya zanta da ‘yan jaridan, mazauna kauyen sun shiga halin lahaula a lokacin da aka kawo harin.

Gwamnan Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara Hoto: hausa.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bayan wadanda aka yi awon-gaba da su, mazaunin yace mutane da yawa sun samu rauni.

A cewarsa, an dauki Mai garin da sauran wadannan mutum shida ne a gidajensu, daga nan aka wuce da su zuwa sansanin ‘yan bindiga.

Babu zaman lafiya a Zurmi

“Yanzu haka mu na rayuwa cikin dar-dar domin ‘yan bindiga su na yawon kawo mana hari, su dauki mutane, su nemi kudin fansa.
Ba da dadewa ba ‘yan biniga suka dauke mana mutane 10 a gonakinsu, har yanzu su na hannunsu domin an gagara fanso su.”

Kara karanta wannan

Manoma sun huta, sojoji sun sheke wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a Zamfara

- Dahiru Amadu

Rahoton yace ba a iya samun kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu domin jin ta bakinsa game da harin ba.

Ana samun sauki - NSA

An ji labari sababbin salon da sojoji da sauran dakarun tsaro suka dauka yana taimakawa wajen yakar ‘yan ta’adda da tsageru a Najeriya.

A wajen wani taro da Hukumar DIA ta shirya a Abuja, aka ji Mai ba Shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Babagana Munguno ya fadi haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel