2023: Kwankwaso Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Kungiyar IPOB Idan Ya Zama Shugaban Kasa

2023: Kwankwaso Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Kungiyar IPOB Idan Ya Zama Shugaban Kasa

  • Dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso ya sake bayyanawa yan Najeriya yadda zai magance rashin tsaro a kasar
  • Da ya ke tsokaci kan shirinsa idan an zabe shi shugaban kasa a zaben 2023, Kwankwaso ya ce zai tattauna da IPOB da sauran kungiyoyin masu tada kayan baya don dawo da tsaro a kasar
  • A bangare guda, kasar na cigaba da fama da kallubalen rashin tsaro wanda ke cigaba da zama barazana ga yan Najeriya

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso ya ce zai tattauna da yan haramtaciyyar kungiyar IPOB da sauran kungiyoyin masu tada kayan baya 'don dawo da zaman lafiya' dan an zabe shi shugaban kasa.

A hirar da ya yi da Daily Trust, tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce zai iya yin sulhu da kungiyar masu tada kayan bayan kuma zai yi hadin gwiwa da kasashen waje don tabbatar da tsaro ya dawo yankin.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Kwankwaso
2023: Kwankwaso Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Kungiyar IPOB Idan Ya Zama Shugaban Kasa. @KwnkwasoRM
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zan tattauna da kungiyoyin masu tada kayar baya - Kwankwaso

Kwankwaso ya ce zai kara yawan yan sanda da sojoji daga 230,000 da 250,000 a halin yanzu zuwa miliyan daya domin kawo karshen rashin tsaro a kasar kamar yadda ya taba fada yayin taron yin muhawara, rahoton Arise TV.

Ya ce zai kuma yi amfani da fasahar zamani domin yaki da yan bindiga, yan ta'adda da kungiyoyin masu neman ballewa daga kasa kamar yadda kuma zai tattauna da kungiyoyin yan bindigan.

Kwankwason ya ce:

"Ba wai kawai a samar da zaman lafiya a Najeriya bane, idan kana da zaman lafiya a Najeriya amma makwabtanta ba su da zaman lafiya, za mu samu matsala. Shi yasa ba iyaka zaman lafiya a kasar muke kallo ba."

A bangare guda, IPOB na cigaba da neman a bata damar ballewa da sashin kudu maso gabashin kasar daga Najeriya inda Ibo ne mafi yawanci.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya fusata, ba ya son sake jin labarin tsageru a gangamin kamfen 2023

Amma, hukumomi a Najeriya su ayyana kungiyar na Nnamdi Kanu wanda a halin yanzu ya ke tsare a matsayin kungiya ta ta'addanci.

2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

A wani rahoton, mutane hudu cikin yan takarar za su yi fafata a zaben 2023 karkashin jam'iyyar NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Yan takarar, sune Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Asali: Legit.ng

Online view pixel