Hadimin Gwamna Ya Yi Murabus kan Rashin Samun Albashi na Tsawon Shekara

Hadimin Gwamna Ya Yi Murabus kan Rashin Samun Albashi na Tsawon Shekara

  • Mai taimakawa gwamnan Benue kan harkokin matasa da yaɗa labarai ya yi murabus kan matsalar rashin albashi
  • Bayan murabus ɗinsa, Atu Joseph ya yi zargin cewa ya yi aiki tsawon watanni ba tare da karɓar albashi ko alawus ba
  • Murabus din nasa ya haifar da hasashen sauya sheƙar siyasa, musamman bayan ziyararsa ga George Akume kafin murabus ɗin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Hadimi na musamman ga gwamnan Benue, Alia Hyacinth kan harkokin matasa da yaɗa labarai, Atu Terver Joseph, ya yi murabus.

Joseph ya yi murabus daga muƙaminsa ba tare da bata lokaci ba, yana mai bayyana cewa ya ɗauki matakin ne saboda dalilai na ƙashin kansa.

Hadimin gwamna ya yi murabus kan albashi
Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue yana jawabi a taro. Hoto: Fr. Alia Hyacinth.
Source: Twitter

A cikin wasiƙar murabus da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Benue, Atu ya gode wa Gwamna Hyacinth Alia bisa damar da aka ba shi ta yin aiki a gwamnatinsa, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya dawo da zaman lafiya a wasu yankuna': Matawalle ya hango nasara a 2027

Tsohon hadimin gwamna ya godewa mai gidansa

Joseph ya godewa gwamnan bisa damarmaki da ya ba shi inda ya ce ya samu kwarewa ta fannoni da dama.

Ya ce:

"Cikin girmamawa da godiya nake miƙa murabus daga muƙamina na Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan harkokin matasa da yaɗa labarai, wanda zai fara aiki nan take."

Ya ƙara da cewa yana matuƙar godiya da damar yin aiki ƙarƙashin gwamnatin Alia, tare da yaba masa saboda amincewar da ya nuna masa.

Atu ya ce ya samu ƙwarewa mai yawa yayin gudanar da aikinsa, sannan ya yi wa gwamnan fatan samun nasara a ci gaba da hidimtawa al'ummar Benue.

Sai dai bayan murabus ɗin, tsohon hadimin ya fitar da saƙon bidiyo inda ya yi zargin cewa ya yi shekara ta farko a aikinsa ba tare da karɓar albashi ko alawus ba.

Ya ce:

"Na yi aiki a shekara ta farko bayan wannan naɗi ba tare da albashi da alawus ba, amma duk da haka na ci gaba."

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya tona bakar magana da Obi ya fada game da Atiku a sirrance

Hadimin gwmana ya sauka daga kujerarsa a Benue
Taswirar jihar Benue daga Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda hadimin gwamna ya sha wahala a Benue

A cewarsa, sai bayan cikar shekara guda da naɗinsa ne ya fara karɓar albashi daga gwamnatin da yake yi wa aiki, cewar rahoton TheCable.

Har ila yau, Atu ya yi nuni da yiwuwar sauya sheƙar siyasa, bayan ya bayyana cewa ya kai ziyara ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, kafin murabus ɗinsa.

Wannan lamari ya jawo hasashe daga masu sa ido kan siyasa cewa tsohon mataimakin na iya sauya sansanin siyasa bayan ficewarsa daga gwamnatin Alia.

Koƙarin jin ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Sir Tersoo Kula, da Mai Ba da Shawara kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Cif Solomon Iorpev, bai yi nasara ba.

Gwamnan Benue zai ba manoma taki mai rahusa

A wani labarin, an ji cewa manoma za su samu taki a farashi mai rahusa bayan tallafin da gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, domin gudanar da noma.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya kare kansa da aka tsoma shi a matsalar sace dalibai a Oyo

Gwanna Hyacinth Alia ya rage farashin takin zamani ga manoma inda a yanzu za su biya N28,000 kan kowane buhu.

Ya bukaci mutanen da za su jagoranci aikin da su gudanar da shi cikin gaskiya da rikon amana ba tare da karkatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.