Abu Hassan: Sojojin Najeriya Sun Sheƙe Babban Kwamandan Boko Haram Da Mayaƙansa 13 A Borno

Abu Hassan: Sojojin Najeriya Sun Sheƙe Babban Kwamandan Boko Haram Da Mayaƙansa 13 A Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Abu Hassan
  • Sojojin Operation Hadin Kai sun halaka Abu Hassan da mayakansa ne yayin wani artabu da suka yi a Mafa yayin da suke sintiri
  • Dakarun sojojin sun jiyo maganganu tsakanin yan ta'addan inda wani ke magana da wani kwamandan ya sanar da shi Abu Hassan ya 'mutu'

Borno - An rahoto cewa dakarun sojojin Najeriya na operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe kwamandan Boko Haram a ranar Talata.

An kashe kwamandan mai suna Abu Hassan ne tare da wasu yan ta'adda guda 13, The Cable ta rahoto.

Taswirar Borno
Sojojin Najeriya Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram, Abu Hassan, Da Mayakansa 13 A Borno. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Zagazola, wata jarida mai kawo rahotanni kan ta'addanci, an kashe yan ta'addan ne yayin da sojoji da ke sintiri a yankin Mafa suka bude wa yan ta'addan da ke kokarin tserewa wuta.

Kara karanta wannan

Luguden NAF Ya Halaka Manyan Yan Bindiga 3 da Ake Nema da Mayankansu a Jihohin Arewa

Jami'an Tsaro Sun Jiyo Dan Ta'adda Na Tabbatar Da Mutuwar Abu Hassan

An rahoto cewa an jiyo daya cikin yan ta'addan yana magana da wani kwamanda a wani sansani na Abu Iklima, yana cewa sojojin sun kashe yan Boko Haram da dama har da Abu Hassan, kwamandansu.

An ambato dan ta'addan na cewa:

"Wani ya bude mana wuta yayin da muke janye wa daga filin daga a Ngowom. Muna kan hanyarmu da gawarwakin. Muna zuwa Gaizuwa.
"Abu Hassan ya yi barci (mutu), wasu cikin mayakan mu kuma sun jikkata, akwai yiwuwar mu bukaci magani na gaggawa. Don Allah ka kasance cikin shiri."

Hakan na zuwa ne makonni bayan dakarun Operation Hadin kai sun kashe yan ta'addan Boko Haram shi a jihar ta Borno.

An ce an kashe yan ta'addan ne yayin sintiri inda aka kai samame mabuyarsu da ke kan hanyar Kumshe-Banki a Borno.

Sojoji Najeriya Sun Kashe ’Yan Ta’adda da Dama a Jihar Kaduna

Kara karanta wannan

'Yan Zamfara sun tona moboyar su Turji yayin da sojoji ke neman 'yan ta'adda ruwa a jallo

A wani rahoton kuma, rundunar sojin Najeriya na sashe na 1 da a jihar Kaduna sun share yankunan Maidaro, Kagi Hill, Kusharki da Anguwan Madaki a karamar hukumar Birnin Gwari daga 'yan ta'adda.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, birgediya janar Onyema Nwachukwu ya fitar, inda yace an kashe 'yan bindiga hudu kana wasu da dama sun tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel