'Yan Bindiga Sun Aike da Sako, Sun Yi Barazanar Tilasta Wa Gwamna Soludo Yin Murabus

'Yan Bindiga Sun Aike da Sako, Sun Yi Barazanar Tilasta Wa Gwamna Soludo Yin Murabus

  • Yan ta'adda sun yi barazanar zafafa kai hare-haren ta'addanci a Anambra domin matsa wa gwamna Soludo ya yi murabus
  • A wani sakon murya dake yawo, wani kwamandan ESN yace tun da gwamnan ya zaɓi farautarsu da jami'an tsaro to zasu ɗau mataki
  • ESN ita ce tsagin mayaƙan kungiyar 'yan aware dake fafutukar kafa ƙasar Biafara a kudu maso gabashin Najeriya

Anambra - Wasu miyagu da ake zaton mambobin haramtacciyar ƙungiyar ESN ne sun yi barazanar tilasta wa gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya yi murabus ta hanyar zafafa kai hare-hare.

Sun yi gargaɗin cewa tun da ya zaɓi amfani da dakarun 'yan sanda da Sojoji wajen farautarsu, to zasu tada hankalin jihar ta yadda ba zai iya shugabanci ba.

Gwamna Soludo na jihar Anambra.
'Yan Bindiga Sun Aike da Sako, Sun Yi Barazanar Tilasta Wa Gwamna Soludo Yin Murabus Hoto: thenation
Asali: Facebook

A wani sakon murya ta ɗaya daga cikin hatsabibin yan ta'addan wanda ya bayyana sunansa da 'Okwute' (Kwamandan ESN na Awka ta kudu da arewa), wanda The Nation ta samu, ya yi barazanar ci gaba da kashe-kashe a jihar.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Kwankwaso Ya Fallasa Asirin Gwamnoni na Satar Dukiyar Talakawa

Jagoran ESN ɗin ya kuma yi barazanar cewa zasu kai hari Asibitin wani kwararren likita kuma zasu kashe kowa dake wurin idan ya musu gardama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meya haɗa su da Likitan?

Haka nan ya yi ikirarin cewa sun sa ido kan al'amuran Likitan da kuma harkokinsa a garin, sun gano cewa baya goyon bayan fafutukarsu ta kafa Biafara.

A cewarsa, "Shin ka yi imani da kafa Biafara? Nawa ka taba ba da gudummuwa a fafutukar tun farkon farawa? Wasu daga cikinku na kokarin zagon kasa ga kokarin da muke yi a ƙasar Igbo."

"Nawa zaka bayar na taimakawa aikin da muka sa a gaba? Zamu turo Asusun Banki ka tura mana N500,000 ko kuma ka barshi kawai.."

Bayanai sun nuna cewa yayin da Likitin da yake magana a kai ya yi alƙawarin tura musu N20,000, kwamandan ESN cikin fushi ya yi barazanar tasar Asibitinsa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

2023: Bayanai Sun Fito, Abinda Gwamnan Bauchi Ya Faɗa Wa Ortom Kan Kalaman Fulani da Atiku

"Tunda gwamna Soludo ya sha alwashin farautarmu da 'yan sanda da Sojoji a jihar nan, zamu rikita Anambra ta yadda zatai masa wahalar shugabanci kuma zamu wajabta masa ya yi murabus," inji muryar.

Shin yan sanda sun samu rahoto kan batun?

Amma jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, wanda ya bukaci a bari ya saurari muryar, ya shawarci duk me sakon muryar ya kai Caji Ofis mafi kusa.

Kai rahoton muryar a cewar kakakin yan sandan zai basu damar gudanar da bincike a tsanake.

A wani labarin kuma Wasu yan bindiga sun kai mummunan hari shingen binciken ababen hawa na yan sanda a Anambra

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun buɗe wa mutane wuta lamarin da ya haddasa gudun neman tsira a yankin Ihiala.

Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayuwarsu sakamakon harin, jami'an tsaro sun maida martani anyi musayar wuta a wurin.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Daga Cikin Gwamnonin Tsagin Wike Na Shirin Yaudararsa, Zasu Koma Bayan Atiku

Asali: Legit.ng

Online view pixel