'Yan Bindiga Sun Bukaci N40m Kan Yara 20 Da Aka Sace A Neja

'Yan Bindiga Sun Bukaci N40m Kan Yara 20 Da Aka Sace A Neja

  • Yan bindiga da suka yi garkuwa da kananan yara guda 20 daga garin Kusherki a karamar hukumar Neja sun nemi kudin fansa
  • Bayan kananan yaran sun shafe kimanin kwana 20 a hannun maharan, sun nemi a biya su Naira miliyan 40 kafin su sako su
  • Mr Emmanuel Umar, Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyukan jin kai na jihar Neja ya ce gwamnati na jami'an tsaro na iya kokarinsu don ceto yaran

Jihar Neja - Yan bindiga, wadanda suka sace yara 20 daga Kusherki a karamar hukumar Rafi na jihar Neja, suna bukatar Naira miliyan 40 kafin su sake su, rahoton Vanguard.

Yaran, wanda aka ce suna tsare tsawon kimanin kwana 20, shekarunsu tsakanin 4 ne zuwa 10.

Taswirar Neja
'Yan Bindiga Sun Bukaci N40m Kan Yara 20 Da Aka Sace A Neja. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Wani mazaunin garin, Auwal Usman, a hirar wayar tarho a ranar Talata ya ce kananan yaran na fuskantar wahalhalu a hannun wadanda suka sace su.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Arewa yayin da 'yan bindiga suka sace wani Limamin Katolika

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Yaran nan kanana ne sosai kuma ba su iya kula da kansu. Shekarunsu tsakanin 4 zuwa 10 ne."

Usman ya kara da cewa a cikin yaran akwai maza hudu da mata 16.

Muna iya kokarin mu don ceto su - Emmanuel Umar

Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyukan jin kai na jihar Neja, Mr Emmanuel Umar ya ce gwamnatin jihar na duk mai yiwuwa don ganin ta ceto yaran ba tare da wani abu ya same su ba.

Ya kara da cewa:

"Gwamnatin jihar na yin duk abin da za ta iya don tabbatar an sada yaran da iyalansu ba tare da wani abu ya same su ba.
"Hukumomin tsaro suma suna yin iya kokarinsu kuma mun tabbata cewa za mu yi nasara daga karshe."

Masu Garkuwa Sun Fada Komar Yan Sanda Yayin Da Suke Kokarin Karbar Cikon Kudin Fansa A Wata Jihar Arewa

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Yan sanda a jihar Gombe sunyi holen wani Mohammed Aminu da Salisu Sa'idu, wadanda aka kama yayin karban kudin fansa N300,000 daga iyalan wadanda suka sace.

A cewar mai magana da yawun rundunar yan sanda, Mahid Abubakar, hakan na zuwa ne bayan tawagar masu garkuwar sun karbi N100,000 bayan sace wani Jibrin Muhammad a Jihar Taraba.

Makwogoron yan sandan ya bayyana cewa tawagar binciken manyan laifuka, SCID ne ta kama Sa'idu a Kano yayin bincike, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel