Yadda Yan Bindiga Sun Kashe Malami, Shugaban Matasa Da Wasu Mutum 2 A Kaduna

Yadda Yan Bindiga Sun Kashe Malami, Shugaban Matasa Da Wasu Mutum 2 A Kaduna

  • Yan bindiga sun halaka wani malamin makaranta da shugaban matasa da wasu mutane biyu a Kaduna
  • Lamarin ya faru ne a kauyukan Gefe da Tudun Mare a karamar hukumar Kajuru na jihar ta Kaduna
  • Wani mazaunin Tundun Mare mai suna Elisha Arziki ya magantu kan harin ya ce an birne shugaban matasan a ranar Litinin

Jihar Kaduna - Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun kashe mutum hudu a wani kauye ciki har da wani sabon malami a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna, Daily Trust ta rahoto.

Kashe-kashen sun faru ne a wasu garuruwa masu suna kauyen Gefe da Tudun Mare a karamar hukumar na Kajuru.

Taswirar Kaduna
Yan Bindiga Sun Kashe Malami, Shugaban Matasa Da Wasu Mutum 2 A Kaduna. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Jama’ar Ngala da N255m, Kayan Abinci da Sutturu

Harin ya yi sanadin rayyuka uku ciki har da wani shugaban matasa a daren ranar Lahadi.

Mazaunin garin ya magantu kan harin

Within Nigeria ta tattaro cewa a harin na biyu a Tudun Mare ne aka kashe wani malami mai suna Elisha Arziki aka kashe.

Wani mazaunin mazaunin garin mai suna Benjamin, ya ce an birne shugaban matasan da wasu mazauna kauyen biyu a ranar Litinin.

Ya ce:

"Yan bindigan sun kashe shugaban matasan da wasu mazauna kauyen biyu lokacin da suka kawo hari a ranar Lahadi. An birne su a ranar Lahadi. Yan bindigan kuma sun kashe wani malami a kauyen Tudun Mare a daren ranar Litinin."

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya yi alkawarin zai kira wakilin majiyar Legit.ng ya bada karin bayani amma bai kira ba har lokacin hada wannan rahoton.

Sojoji Sun Saki Sunaye Da Hotunan Shugabannin 'Yan Ta'adda 19 Da Ake Nema Ruwa A Jallo, Tare Da Tukwicin N5m

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Bindige Dan Sa-kai Da Wasu Mutane 4 a Wata Jahar Arewa

A wani rahoto, hedkwatar tsaron Najeriya, ta fitar da sunayen kwamandojin yan ta'adda 19 da ke adabar yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a kasar, rahoton Daily Trust.

Hedkwatar tsaron ta ce za ta ba'ada tukwicin Naira miliyan 5 ga duk wani dan Najeriya da ya taimaka da bayanan yadda za a kama yan ta'addan, ta bukaci al'umma su tuntube ta a wannan lambar 09135904467.

Ta ce hakan ya zama wajibi ne domin cigaba da kawar da abokan gaban, inda ta kara da cewa hakan yunkuri ne na dawo da zaman lafiya gaba daya a kasar, rahoton LIB.

Asali: Legit.ng

Online view pixel