Birtaniya Ta Yi Ƙarin Haske Kan Shirin Ƴan Ta'adda Na Kai Hari Abuja, Ta Lissafa Jihohi 12 Da Ya Dace A Gujewa

Birtaniya Ta Yi Ƙarin Haske Kan Shirin Ƴan Ta'adda Na Kai Hari Abuja, Ta Lissafa Jihohi 12 Da Ya Dace A Gujewa

  • Ofishin jakandancin Birtaniya, kasashen rainon Birtaniya da cigaba, FCDO, ta sabunta shawarwari da ta bada ga tafiye-tafiye a Najeriya
  • A sabbin shawarwarin da ta bada, FCDO ta ce bata bada shawarar yin tafiya zuwa Abuja, sai dai wanda ya zama wajibi
  • Duk da hakan, FCDO ta gargadi cewa har yanzu akwai barazanar yiwuwar yan ta'ada su kai hari a Najeriya, kuma ta yi gargadin zuwa wasu jihohi

FCT, Abuja - Birtaniya a sabunta shawarwarin tafiye-tafiye da ta bawa yan kasarta a Najeriya, tana mai cewa kada a tafi Abuja sai dai kawai idan ya zama wajibi.

Ofishin jakandancin Birtaniya, kasashen rainon Birtaniya da cigaba wato FCDO ya bayyana hakan ne a shawarwarin tafiye-tafiye da ya wallafa a shafinsa a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Lokacin Cigaba da Sufurin Jirgin Kasa a Titin Kaduna-Abuja

Kofar Birnin Abuja
Birtaniya Ta Yi Ƙarin Haske Kan Shirin Ƴan Ta'adda @SaharaReporters.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng ta tunatar da cewa Birtaniya da Amurka sun yi gargadin babban harin "ta'addanci" a birnin tarayya Abuja, inda suka bukaci yan kasarsu su guji zuwa birnin idan ba ya zama dole ba.

Har yanzu akwai barazanar, in ji Birtaniya cikin sabuwar gargadi kan tafiye-tafiye

Duk da cewa mahukunta na Birtaniya sun ce yan kasar na iya zuwa Abuja, sunyi gargadin har yanzu akwai barazanar kai harin a birnin tarayyar.

Sanarwar ta ce:

"Yanzu FCDO bata bada shawarin yin tafiya zuwa birnin tarayya Abuja sai dai na wajibi, kuma har yanzu akwai barazanar, kuma an yi karin bayani kan barazanar kawo harin ta'addanci a yankin.
"Shawarar da FCDO ta bada na hana yin tafiya zuwa wasu wurare har yanzu yana nan."

Jihohin da aka shawarci yan Birtaniya kada su tafi

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

  1. Jihar Borno
  2. Jihar Yobe
  3. Jihar Adamawa
  4. Jihar Gombe
  5. Jihar Kaduna
  6. Jihar Katsina
  7. Jihar Zamfara
  8. Jihar Delta (yankunan ruwa)
  9. Jihar Bayelsa (yankunan ruwa)
  10. Jihar Rivers (yankunan ruwa)
  11. Jihar Akwa Ibom (yankunan ruwa)
  12. Jihar Cross Rivers (yankunan ruwa)

Jihohin da yan Birtaniya za su iya zuwa kawai don ayyuka masu muhimmanci

  1. Jihar Bauchi
  2. Jihar Kano
  3. Jihar Jigawa
  4. Jihar Neja
  5. Jihar Sokoto
  6. Jihar Kogi
  7. kilomita 20 na iyakokin Niger a Jihar Kebbi
  8. Jihar Abia
  9. yankunan da ba ruwa a jihohin Delta, Bayelsa da Rivers
  10. Jihar Plateau
  11. Jihar Taraba

Shawarar tafiye-tafiye: Akwai yiwuwar yan ta'adda za su kawo hari a Najeriya, in ji Birtaniya

Birtaniya, har yanzu ta ce akwai yiwuwar yan ta'adda su kawo hari a Najeriya, tana mai cewa barazanar ya karu a 2022.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Mafi yawancin hare-haren da Boko Haram ko ISWA ke kaiwa na faruwa ne a jihohin Borno, Yobe da Adamawa a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Ta'adda Suna Shirin Kai Hari Amurka, Birtaniya Ta Yi Gargadi

"Akwai kuma wasu hare-haren a wasu jihohi kamar Gombe, Kano, Kaduna, Plateau, Bauchi da Taraba.
"Barazanar kai harin a Najeriya ya hada da babban birnin tarayya, Abuja, da kewaye. Barazanar ya karu a 2022."

Bayan Amurka, Manyan Kasashen Duniya 3 Sun gano Yiwuwar kai hari a Birnin Abuja

Hukumomi a kasashen Kanada da Australiya sun gargadi mutanensu kan yin zuwa Najeriya saboda fargabar harin ta'addanci.

Wannan gargadin na zuwa ne a kimanin kwanaki uku bayan Amurka da Birtaniya sun ce sun gano barazanar rashin tsaro a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel