Yan Sanda Sun Kama Dagacin Kauyen Katsina Bisa Hada Baki Da Yan Ta'adda Don Kashe Wani Manomi

Yan Sanda Sun Kama Dagacin Kauyen Katsina Bisa Hada Baki Da Yan Ta'adda Don Kashe Wani Manomi

  • Yan sanda a jihar Katsina sun kama dagacin kauyen Gobirawa a karamar hukumar Faskari, Surajo Madawaki kan zargin hada baki don kashe wani manomi Yahaya Danbai
  • Danbai ya halaka wani dan ta'adda da ya kawo masa hari a gonarsa da AK 47, daga bisani ya kaiwa dagaci rahoto ya mika masa bindigan
  • Shi kuma dagacin sai ya kira shugaban yan bindiga Hamisu ya mayar masa da bindigan, shugaban yan bindigan ya kashe Danbai ya kuma kakabawa garin harajin N10m

Jihar Katsina - Yan sanda a jihar Katsina sun kama wani dagacin kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Faskari kan zargin hada baki da yan ta'adda, The Cable ta rahoto.

Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah, ya yi holen wanda ake zargin gaban manema labarai a ranar Juma'a, tare da wasu da ake zargin.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

suspects in Katsina
Yan Sanda Sun Kama Dagacin Kauyen Katsina Bisa Hada Baki Da Yan Ta'adda Don Kashe Wani Manomi. Hoto: PM News.
Asali: Facebook

Ya ce yan sandan sun samu kiran neman dauki daga wani Yahaya Danbai, dan shekara 35, cewa wani da ake zargin dan ta'adda ne ya kawo masa hari a gonarsa da bindiga AK 47.

Mr Isah ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Manomin ya yi jarumta, ya ci galaba kan maharin, ya kwace bindigarsa, ya kuma halaka dan ta'addan.
"Ya dauki bindigar ta AK 47 ya kai rahoto wurin mai unguwa, Malam Surajo Madawaki, mai shekaru 50.
"A maimakon sanar da yan sanda, dagacin ya kira wani Hamisu, hatsabibin shugaban dan ta'addan da aka kashe ya mika masa AK 47 din da aka kwato.
"Daga nan, Hamisu ya tattaro yaransa, suka zagaye kauyen, suka fito da jarumin manomin suka kashe shi nan take."

Shugaban dan ta'addan ya kakabawa kauyen biyan N10m

PM News ta rahoto dan ta'addan ya kuma ci kauyen harajin N10m kan kashe masa dan tawagarsa, idan kuma ba a biya ba zai kashe kowa a kauyen.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cafke Dagacin Kauyen Dake Hada Kai da ‘Yan Bindiga a Katsina

Ya ce:

"Tun lokacin dagajin kauyen ya boye har sai lokacin da aka kama shi.
"A yayin bincike, dagajin kauyen ya amsa wa yan sanda laifin da ake tuhumarsa."

Kakakin yan sandan ya kara da cewa yan sandan sun kama wasu bata gari ciki har da masu leken asiri, barayin mota da barayin shanu.

Sokoto: An Kama Dagajin Kauye Kan Dillancin Wiwi Da Miyagun Kwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa NDLEA ta ce ta kama dagajin kauyen Ruga, a karamar hukumar Shagari kan laifin sayar da muggan kwayoyi, Daily Trust ta rahoto.

Kakakin rundunar ta NDLEA ya ce an kama Alhaji Umaru Mohammed wanda aka fi sani da Danbala ne a ranar 22 ga watan Agustan 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel