Sojoji Sun Bindige Kwamandojin IPOB 13, Sun Kwato Makamai Da Kayayyakin Aikin INEC

Sojoji Sun Bindige Kwamandojin IPOB 13, Sun Kwato Makamai Da Kayayyakin Aikin INEC

  • Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe kwamandojin IPOB a kalla guda 13 a yankin kudu maso gabas
  • Sojojin kuma sun yi nasarar kwato kayayyaki kamar bindigu, harsashi, babura, kayan sojoji, kayan aikin INEC da wasu abubuwan
  • Direktan watsa labarai na rundunar sojoji, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya sanar da hakan a ranar Alhami a Abuja

FCT, Abuja - Dakarun sojojin Najeriya sun kashe a kalla kwamandojin haramtaciyar kungiyar IPOB da ESN guda 13 kan laifuka da suke yi a kudu maso gabas, rahoton Daily Trust.

Sojojin sun kuma kwato kayayyakin rajistan zabe mallakar hukumar zabe mai zaman kanta INEC da wasu kayayyakin.

Dakarun sojojin Najeriya
Sojoji Sun Bindige Kwamandojin IPOB 13, Sun Kwato Makamai Da Kayayyakin Aikin INEC. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Manjo Janar Musa Danmadami, direktan watsa labarai na sojoji ya sanarwa manema labarai hakan a Abuja a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Miyetti Allah Ta Roki CBN Ya Kara Wa'adi Saboda Kada Fulani Suyi Hasara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Danmadami ya yi bayanin cewa rundunar sojojin tare da sauran hukumomin tsaro domin cigaba da magance barnar da kungiyoyin bata gari ke yi don musgunawa mutanen yankinsu, Daily Trust ta rahoto.

Abubuwan da sojoji suka kwato daga hannun yan IPOB/ESN

Ya ce:

"Cikin satin da ake dubiya, dakarun sojoji sun kashe bata garin yan IPOB/ESN guda 13, an kama masu magani guda shida.
"Dakarun sun kuma kwato AK-47 bakwai, kananan bindiga kirar gida, sniper rifle, pump action gun, harsashi 15 masu tsawon 7.62mm, harashi 13 masu tsawon 7.62mm NATO, harashi takwas 9mm da wasu harsasan biyar.
"Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da takalman sojoji uku, kayan sojoji biyu da kuma hulunan sojoji biyu."

Ya cigaba da cewa:

"An kuma kwato kyamaran CCTV biyu, na'urar daukan hoto na INEC daya, akwatin INEC daya, wayar walkie talkie, rediyo, na'urar sola, babur, motocci da wasu abubuwa.

Kara karanta wannan

Jerin Bukatu 7 Da CAN Ta Gabatarwa Tinubu: Bukatu 2 Da Zai Yiwa Tinubu Wahalan Biya

"An mika dukkan abubuwan da aka kwato daga wurin bata garin zuwa hukumomin da suka dace don daukan mataki."

Sojoji Sun Kashe Wani Dansanda Bayan Sun Lakada Mishi Dukan Tsiya A Legas

A wani rahoton, wasu fusatattun sojoji sun lakada wa wani dan sanda duka inda suka kashe har lahira a wani hari da suka kai kan babbar hanyar Mile 2 Badagry a jihar Legas a ranar Laraba.

Rahoton Daily Trust Dan sandan da ya rasu ya kasance Insifeto ne da ke aiki da sashen Ojo na rundunar ‘yan sandan jihar Legas.

Sojoji ne suka kai wa jami’in da abokan aikinsa hari a lokacin da suke gyarar cunkoson ababen hawa a kan babbar hanyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel