Fargaba Yayin Da Yan Sanda Suka Mamaye Ginin Majalisar Wata Fitacciyar Jiha A Najeriya

Fargaba Yayin Da Yan Sanda Suka Mamaye Ginin Majalisar Wata Fitacciyar Jiha A Najeriya

  • Ana zaman dar-dar yayin da jami'a yan sanda suka mamaye harabar ginin majalisar jihar Ekiti a yau Laraba, 16 ga watan Nuwamba
  • An hangi ma'aikatan majalisar suna ta fitowa daga ofisoshinsu suna kama hanyar komawa gidajensu a yayin da yan sandan ke sintiri a harabar majalisar
  • Gboyega Aribisogan, sabon zababben kakakin majalisar ya ce hedkwatar yan sanda ta sanar da cewa ta samu bayanin sirri da ke nuna bata gari na shirin kawo hari majalisar

Ado Ekiti - An rufe majalisar jihar Ekiti saboda rahotannin cewa wasu yan daba da ba a san ko su wanene ba za su kawo hari.

Vanguard ta rahoto cewa an girke yan sanda a wurare masu muhimmanci a harabar majalisar don hana kutse da tabarbarewar doka da oda.

Majalisar Ekiti
Yan Sanda Sun Mamaye Ginin Majalisar Wata Fitacciyar Jiha A Najeriya. Hoto: @VanguardNGR
Asali: Twitter

PM News ta rahoto cewa an kuma hangi ma'aikatan majalisar suna fitowa daga ofisoshinsu suna tafiya gidajensu.

Kara karanta wannan

Luguden NAF Ya Halaka Manyan Yan Bindiga 3 da Ake Nema da Mayankansu a Jihohin Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan sanda sun fada mana yan daba na shirin kawo hari majalisar Ekiti - Aribisogan

A hirar da aka yi da wasu cikin ma'aikatan da suka nemi a boye sunansu, sun yi bayanin cewa hedkwatar yan sanda ta bada umurnin ma'aikatan majalisar su fice saboda zaman lafiya, tana mai cewa wasu na shirin kawo hari majalisar jihar.

Sabon zababben kakakin majalisar Rt. Hon. Gboyega Aribisogan, a hirar wayar tarho da menema labarai, ya ce babu rikici a majalisar.

A cewar Aribisogan:

"Shugabannin yan sanda reshen Ekiti sun sanar da mu a safiyar yau cewa suna da bayannan sirri sahihi da ke nuna cewa wasu yan daba za su kawo hari majalisar kuma don kiyaye tarbarbarewar doka da oda, akwai bukatar su turo jami'ansu kuma sunyi alkawarin yin bincike kan lamarin su bamu rahoto kafin tashi aiki a yau.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mambobin Majalisa Sun Naɗa Sabon Kakaki A Jihar da APC Ke Mulki

"Ina kira ga takwarori na da ma'aikata su yi hakuri, nan bada dadewa ba komai zai koma yadda aka saba."

Idan za a iya tunawa a zabi Aribisogan a matsayin sabon kakakin majalisa ne a jiya bayan kayar da Misis Olubunmi Adelugba daga Emure Ekiti.

Yan Daba Ɗauke da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku a Kaduna

Rahotonni sun nuna cewa yan daba sun farmaki magoya bayan PDP a Ranches Bees Stadium, Kaduna, wurin gangamin taron ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rubutu da ya saki a shafinsa na Facebook ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel