Rokar Dakarun NAF ta Halaka Kwaya da Mainoka, Manyan Shugabannin ISWAP a Yankin Tafkin Chadi

Rokar Dakarun NAF ta Halaka Kwaya da Mainoka, Manyan Shugabannin ISWAP a Yankin Tafkin Chadi

  • Ali Kwaya da Bukar Mainoka, manyan shugabannin majalisar Shura ta ISWAP sun sheka lahira sakamakon roka da bama- bamai da sojin sama suka harba musu
  • An gano cewa sun tattaru da mambobin kungiyar ta’addanci motoci 15 a Bolewa dake yankin Tumbun na tafkin Chadi inda suke shirya yadda zasu kai hari
  • Dakarun sun ga wasu motoci biyu dauke da jigatattun ‘yan ta’addan za a canza musu maboya bayan luguden, amma sun sake harba musu bam

Borno - Manyan shugabannin kungiyar ta’addanci ta ISWAP sun sheka lahira sakamakon luguden wutan da dakarun Operation Hadin Kai suka yi musu a tafkin Chadi.

Rokar NAF
Rokar Dakarun NAF ta Halaka Kwaya da Mainoka, Manyan Shugabannin ISWAP a Yankin Tafkin Chadi. Hoto daga @ZagazOlamakama
Asali: Twitter

Kamar yadda Zagazola Makama suka bayyana, dakarun sun kai farmakin ta jiragen yaki ne a Belowa, daya daga cikin maboyar ISWAP/Boko Haram a Tumbun dake karamar hukumar Abadam a yankin tafkin Chadi.

Ali Kwaya da Bukar Mainoka, manyan shugabannin ISWAP duk sun mutu yayin da wasu mambobi suka jigata sakamakon samamen da aka kai musu ta jiragen yaki.

Kamar yadda majiyar sirri daga rundunar ta bayyana, ‘yan ta’addan na shirya yadda zasu kai hari kan dakarun ne a Bolewa amma aka harba musu roka da bama-bamai a maboyarsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Bayan sa’a daya da kai samamen, ababen hawa biyu dake dauke da ‘yan ta’addan 13 da suka jigata za a kai su wata maboya ta taho amma jiragen NAF sun sake zuba musu ruwan wuta.”

- Majiyar sirri daga sojojin ta sanar.

“Bayanai bayan samamen ya bayyana cewa, shugaban ISWAP Mallam Ali Kwaya wanda babban mamba ne a majalisar Shura da Mallam Bukar Mainoka suna daga cikin wadanda suka rasa rayukansu.”

Sojoji Sun kai Samame Bama

Majiya sirrin ta kara da bayyana cewa sojojin sun kaddamar da makamancin wannan harin a Ngwuri Gana dake karamar hukumar Bama dake gabashin Maiduguri a jihar Borno.

“Samamen ta jiragen yaki sun haifar da nasarori masu yawa bayan bayanan sirri sun tabbatar da cewa kungiyar ‘yan ta’addan a motoci manya 15 an gansu suna tattaruwa a wurin.
“Bayanai daga baya sun bayyana cewa an samu nasarar ruwan wutan ta sama inda aka halaka ‘yan ta’addan masu tarin yawa da dukkan gidajensu kuma ababen hawansu sun kurmushe da wuta.”

- Majiya ta tabbatar.

Kakakin NAF ya Magantu

Edward Gabkwet, mai magana da yawun NAF ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ki bayyana sunayen ‘yan ta’addan da suka rasa rayukansu a yayin harin.

“Mun kama hanyar nasara da yaki da ta’addanci a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma kuma babu ja da baya har sai mun tabbatar dukkan yankunanmu babu ‘yan ta’addan.”

- Gabkwet yace.

“Kada mu manta da cewa jajircewar matukan jiragenmu da sauran ma’aikatanmu inda suke bin umarnin shugaban ma’aikatan tsaron sama, Air Marshal Amao kan cewa ‘yan ta’addan kada su samu maboya, ya zama dole mu kiyaye.”

- Ya kara da cewa.

Yan Sanda Sun Dakile Farmakin da ISWAP ta Kai Caji Ofis a Magumeri, Borno

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta dakile wani farmaki da wasu da ake zargin mambobin ISWAP ne suka kai a birnin Magumeri dake jihar.

Kamar yadda Zagazola Makama, wata wallafa da ta mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi ta bayyana, wadanda ake zargin mayakan ISWAP ne suka tsinkayi caji ofis din ‘yan sanda dake garin a tawagar motocin yaki da babura wurin karfe 12:35 na safiyar lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel