Amurka da Iran na dab da Sa Hannu a kan Yarjejeniyar Kawo Karshen Yaƙin Gabas Ta Tsakiya

Amurka da Iran na dab da Sa Hannu a kan Yarjejeniyar Kawo Karshen Yaƙin Gabas Ta Tsakiya

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ana sa ran sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Iran nan gaba kadan
  • Sai dai kasar Iran ta nuna taka-tsantsan kan lokacin kulla yarjejeniyar, tana mai cewa har yanzu ba a tabbatar da ranar ba tukunna
  • Pakistan, wacce ke taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin, ta ce ana sa ran kammala yarjejeniyar cikin sa'o'i 24 masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa ana sa ran sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2026.

Donald Trump ya bayyana haka ne a lokacin da Iran ke ci gaba da jan kafa, inda ya ce bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, za a bude mashigar ruwa ta Hormuz ga kowa.

Kara karanta wannan

Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran

Amurka da Iran za su kawo karshen yaƙin Gabas ta Tsakiya
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei (hagu) da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Anadolu & Win McNamee via Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton BBC ya bayyana cewa Donald Trump ya ce ana shirin rattaba hannu kan yarjejeniyar nan ba da jimawa ba bayan an kwashe watannibana dauki-ba-dadi.

Iran ta yi martani ga kalaman Donald Trump

Kafar Reuters ta wallafa cewa sai dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya nuna taka-tsantsan kan lokacin kulla yarjejeniyar.

A cewarsa, har yanzu akwai bukatar a jira domin tabbatar da takamaiman ranar sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, yana mai nuni da cewa ba za a kammala hakan nan take ba.

Donald Trump ya yi magana kan sinadarin uranium a Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Trump ya kuma yi magana a kan batun sinadarin uranium da Iran ke tacewa, yana mai cewa idan komai ya daidaita za a dauki matakan da suka dace kan lamarin.

Pakistan ta magantu a kan Amurka da Iran

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa bangarorin da abin ya shafa sun yi kusa da yarjejeniyar zaman lafiya fiye da kowane lokaci.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya ragargaji Iran duk da shirin kulla yarjejeniya

Ya ce idan komai ya tafi yadda ake fata, za a kammala shirye-shiryen yarjejeniyar cikin sa'o'i 24, sannan a sanya hannu ta kafin a fara tattaunawar fasaha a mako mai zuwa.

A ranar Juma'a 12 ga watan Yuni, 2026 ma, ministan harkokin wajen Iran, Seyed Abbas Araghchi, ya ce an kusa cimma matsaya da Amurka a kan kawo ƙarshen yaƙin.

Ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta kunshi sake bude mashigar Hormuz da kuma sassauta wasu takunkuman da Amurka ta kakabawa tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Amurka ta dakatar da kai hari Iran

A baya, kun samu labarin cewa Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa Amurka ta kammala yaƙi da Iran, bayan ya sanar a ranar Alhamis 11 ga watan Yuni, 2026 cewa an cimma matsaya.

Donald Trump ya ce an yi wani babban sulhun da ya ce zai kawo ƙarshen rikicin da ake yi da kasar Iran Da aka shafe tsawon lokaci ana buga wa, da sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz.

Shugaban kasar Amurka ya kara mataimakin shi, JD Vance, na iya halartar bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a Turai cikin kwanaki masu zuwa domin tabbatar da kawo karshen yakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng