Atiku Abubakar
Kungiyar mata ta AYW ta bayyana Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da za ta marawa baya a zaben 2027, tana yabonsa da kwarewa, hangen nesa, da kishin Najeriya.
Fasto Ekong ya hango wani gwamna da zai iya mutuwa kafin 2027, ya bukaci Tinubu ya kula da magoya bayansa, kuma ya shawarci Jonathan da kada ya tsaya takara a 2027.
Atiku da Gudaji Kazaure sun tattauna kan halin da Najeriya ke ciki da matakan ceto ta daga matsaloli, tare da haɗa kai domin samar da jagoranci na gari.
Rahotanni sun ce yunkurin kafa kawancen jam’iyyun adawa domin tunkarar Bola Tinubu a 2027 na fuskantar cikas saboda takarar Atiku Abubakar da batun yanki.
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan hadakar jam'iyyun adawa inda ya ce haɗin gwiwar Atiku, El-Rufai da Obi ba za su iya kayar da APC ba.
Karamin Ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Ata ya caccaki hadakar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i da Peter Obi da adawa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Fadar shugaban ƙasa ta ce yunkurin haɗakar jagororin ƴan adawa irinsu Atiku, Obi da El-Rufai ko a jikin Tinubu domin ya maida hankali wajek sauke nauyi.
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya yi magana kan hadakar Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufa'i domin kifar da Bola Tinubu a zaben 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya yi magana da tsohon gwamnan jihar Rivers kan batun yadda za a janye dokar ta ɓaci a jihar.
Atiku Abubakar
Samu kari