'Yan Bindiga Sun Tafka Ɓarna, Sun Kashe Mai Riƙe da Sarauta a Jihar Kano
- Ana zargin ‘yan bindiga sun kashe basaraken kauyen Taka-tsaba da ke yankin karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano
- Rahoto ya nuna cewa mutane da dama, galibi mata da yara sun tsere daga Zakawa da wasu kauyuka zuwa garin Tsanyawa
- An ce maharan sun sace shanu sama da 100 kafin daga bisani jami'an tsaro su samu nasarar kwato su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ana zargin wasu ‘yan bindiga sun kashe Magajin Garin kauyen Taka-tsaba bayan kai hari kan wasu al'ummomi da ke yankin karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar sun tarwatsa mutane, inda mata da yara suka fara hijira daga kauyuka daban daban zuwa garin Tsanyawa.

Source: Original
An fara bayyana labarin wannan hari ne ta jerin sakonnin da shafin Tsanyawa Reporters ya wallafa a Facebook ranar Laraba da yamma.

Kara karanta wannan
'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya
A daya daga cikin sakonnin, shafin ya ce an kashe Magajin Gari a kauyen Taka-tsaba yayin harin.
Ya ce:
"Lallai mu daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma. Ana zargin ‘yan bindiga sun kashe mai unguwar kauyen Taka-tsaba da ke karamar hukumar Tsanyawa."
Mata da yara sun tsere daga kauyuka
Shafin ya kuma bayyana cewa mata da yara sun fara tserewa daga kauyen Zakawa da sauran kauyukan da ke kusa zuwa garin Tsanyawa bayan maharan sun mamaye yankunansu.
A cewar rahoton:
"A halin yanzu mata da yara na tserewa zuwa garin Tsanyawa daga Zakawa da sauran kauyukan da ‘yan bindiga suka kai hari."
An kwato shanu sama da 100
A wani sabon bayani, shafin ya ce maharan sun kai hari kauyen Zakawa da ke gundumar Yankamaye tare da wani kauye a karamar hukumar, inda suka yi awon gaba da shanu sama da 100.
Sai dai rahoton Leadership ya ce jami'an tsaro sun kai dauki cikin gaggawa, inda suka samu nasarar kwato dukkan shanun da aka sace.
Rahoton ya ce:
"Wakilanmu a yankin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun sace shanu sama da 100. Amma godiya ta tabbata ga Allah, jami'an tsaro sun yi nasarar kwato su. Muna yaba musu tare da addu'ar Allah Ya ci gaba da kare su kuma Ya ba su karfi."

Source: Getty Images
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kokarin jin ta bakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano bai yi nasara ba, domin ba ta fitar da wata sanarwa kan harin a hukumance ba.
Yan bindiga sun sace shugaban makaranta
A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare a ƙaramar hukumar Dekina da ke jihar Kogi yayin da ake gudanar da jarabawar NECO.
Sanarwar yan sanda ta bayyana cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu, shugaban makarantar da kuma wani ma'aikacin wucin gadi na NECO.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kogi, CP Naziru Bello Kankarofi, tare da kwamandan Brigade da mai bai wa gwamnan jihar Kogi shawara kan harkokin tsaro sun kai ziyara makarantar
Asali: Legit.ng
