2027: ADC Ta Ce Gwamnoni 5 na Shirin Shiga Tafiyar Hadaka a Najeriya
- Jam’iyyar ADC da ke jagorantar gamayyar ‘yan adawa ta fara shirin jawo gwamnoni kafin zaben 2027
- Wasu shugabannin PDP daga jihohi daban daban sun fice daga jam’iyyar suka koma ADC domin hada kai da gamayyar
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi sun amince da ADC a matsayin dandali 'yan adawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Jam’iyyar ADC da ke zama dandalin da gamayyar shugabannin adawa ke amfani da shi, ta fara tuntubar wasu gwamnoni da nufin jawo su jam’iyyar kafin babban zaben 2027.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar ADC na amfani da rikicin cikin gida da jam’iyyar PDP ke fama da shi domin jawo wasu gwamnoni na jam’iyyar su sauya sheka zuwa gamayyar.

Asali: Twitter
Wani jigo a jam'iyyar ADC ya bayyanawa jaridar Punch shirin da suke domin jawo gwamnonin da wasu 'yan adawa a hirar da suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzu, shugabanni da dama na PDP daga jihohi daban-daban sun fice daga jam’iyyar tasu suka koma ADC domin hada gwiwa da Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran su.
ADC ta fara shirin jawo gwamnoni 5
Wani babban jigo a jam’iyyar ADC daga jihar Katsina ya ce akwai gwamnoni biyar da suka riga suka bayar da tabbacin za su sauya sheka zuwa ADC bayan kammala rikicin da ke cikin PDP.
Jigon ya ce:
“Gwamnoni biyar daga PDP sun nuna niyyarsu ta shiga ADC, amma suna jiran yadda za a kammala rikici da Nyesom Wike a jam’iyyar kafin su fito fili.
"Wasu daga cikin gwamnoni da ke APC ma suna tare da mu, domin tun watanni 18 da suka wuce muka fara shirye-shiryen gamayyar.”
Wani hadimi ga tsohon minista ya kara da cewa ana tuntubar wasu gwamnoni bakwai daga sassa daban-daban na kasar, duk da cewa bai bayyana sunayen jam’iyyunsu ba.
Tsohon shugaban ADC ya yi magana
Tsohon shugaban jam’iyyar ADC, ya ki bayyana cikakkun bayanai game da gwamnoni da ake niyya su shiga ADC, yana mai cewa wannan lamari ne mai bukatar sirri.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Ba zan iya fadin sunayen gwamnoni da muke magana da su ba. Wannan al’amari ne na sirri sosai. Amma a shirye nake in ba da bayani game da sauran batutuwan gamayyar.”
A farkon watan Yuni, wani jigo a jam’iyyar ADC a jihar Filato, Dr Sani Dawop, ya bayyana cewa akwai gwamnoni shida zuwa bakwai na APC da ke daukar nauyin gamayyar adawa.
Fadar shugaban kasa ta caccaki ADC
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta fusata game da yadda wasu tsofaffin 'yan APC suka shiga ADC.
Mai magana da yawun shugaban kasa ya zargi wasu tsofaffin ministocin Muhammadu Buhari da suka shiga ADC da cewa dama ba su goyon bayan APC dari bisa dari.
Bayo Onanuga ya ce ba wani abu ba ne ya sanya aka shirya hadaka a ADC sai zallar kiyayya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng