2027: An ba Atiku Abubakar da Wasu Jiga Jigan PDP Zaɓi 2 bayan Sun Yi Haɗaka da ADC
- Bode George ya nuna damuwa kan yadda waɗanda PDP ta yiwa riga da wando suka guje ta lokaci guda, suka koma haɗakar jam'iyyar ADC.
- Tsohon mataimakin shugaban PDP ya buƙaci Atiku Abubakar da sauran ƴan jam'iyya da suka rungumi haɗaka su zaɓi ɗaya a tsakanin jam'iyyun biyu
- Ya ce ba zai yiwu su ci gaba da zama a PDP kuma suna yi wa haɗakar ADC aiki ba, inda ya ƙara da cewa ba a haɗa bauta biyu a lokaci guda
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban PDP na Ƙasa, Bode George, ya soki manyan jiga-jigan jam’iyyar da ke cikin tawagar ƴan adawar da ta yi haɗaka a ADC.
George ya gargaɗi Atiku Abubakar da wasu 'yan PDP da ke cikin wannan haɗaka ta ADC su zaɓi ɗaya, ko dai su zauna a PDP ko su tafi haɗakarsu gaba ɗaya.

Asali: Twitter
Bode George ya bayyana haka ne a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin ɗin Channels ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bode George ya ba Atiki da ƴan PDP zaɓi 2
Jigon babbar jam'iyyar adawa ya ce ba zai yiwu su Atiku su zauna a PDP ba kuma a ɗaya ɓangaren, suna aiki tare da haɗakar ADC, rahoton The Cable.
"Ba zai yiwu ka haɗa bauta biyu a lokaci ɗaya ba kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce. Ko dai ka bauta wa A ko B. Amma ka ce kana cikin A da B a lokaci guda, hakan ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
Ya zargi Shugaban jam’iyyar ADC na riko, David, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, cewa suna daga cikin waɗanda suka haddasa rikicin da ya baibaye PDP.
George: 'Bai kamata jiga-jigai su bar PDP ba'
George ya ce haɗakar ADC ba za ta iya zama dandalin adawa kamar PDP ba, domin a cewarsa babu ingantacciyar dabarar aiki ko tsari a cikinta.
“Wannan rashin fahimtar rayuwa ne kawai, me suke nema a can? PDP ce gidanku na asali, ita ce ta ɗaga ku har kuka duk wani matsayi da kuka taka a rayuwa.
"Kun samu ɗaukaka da martaba daga wannan gida, amma saboda wani ƙaramin rikici ne za ku gudu? A’a, ya kamata ku zauna ku gyara."
- Bode George.

Asali: Facebook
An zargi Atiku, Mark da hannu a rikicin PDP
Ya ce wasu daga cikin mambobin haɗin gwiwar ADC su ne suka haifar da rikicin PDP da kansu.
“Lokacin babban taron PDP na ƙarshe da muka yi, Buhari ya gama shekaru takwas, annan Atiku yana so ya tsaya takara, sai muka ce a’a tun da dan Arewa ya gama shekaru takwas, muna da (Peter) Obi daga Kudu.
"Wannan ne ya fara haddasa rikicin. David Mark ne shugaban wannan taron, sai Iyorchia Ayu shi ne shugaban jam’iyyar PDP a lokacin, suka dage a bar Atiku," in ji shi.
PDP ta amince mambobinta su shiga haɗaka?
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta musanta rahoton da ke cewa ta umarci mambobinta su shiga sabuwar jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Sakataren watsa labaran jam'iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya ce har yanzu ba su dauki matsaya kan hadakar ba.
A sanarwar da ya fitar, ya ce yanzu PDP ta mayar da hankali ne wajen dinke duk wata barakar da take fuskanta, tare da hade kan 'ya'yanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng