Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci da Jadawalin Babban Zaben 2027 da INEC Ta Fitar

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci da Jadawalin Babban Zaben 2027 da INEC Ta Fitar

  • Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan jadawalin zaben 2027 da hukumar zaben Najeriya ta tsara
  • Ta ce jadawalin da INEC ta fitar yana da goyon bayan doka karkashin Kundin Dokar Zabe ta shekarar 2026
  • Wannan hukunci da kotun daukaka kara ta yanke ya bai wa hukumar INEC damar ci gaba da aiwatar da jadawalin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya rushe jadawalin gudanar da zaben 2027 da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne ta hannun kwamitin alkalai uku, inda ta amince da karar da INEC ta shigar domin kalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke a ranar 20 ga watan Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

Hotunan jami'a, gidan rediyo da sauran kadarori 46 da aka kwace a hannun Malami

Amupitan
Shugaban hukumr zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Getty Images

Jadawalin INEC yana da karfin doka

Kotun daukaka kara ta ce kotun farko ba ta bi hukunce-hukuncen da suka zama abin koyi ba, tare da bayyana cewa sabon jadawalin zaben da INEC ta fitar wani bangare ne !a Dokar Zabe ta 2026, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ta ce irin wannan jadawali yana da cikakken karfin doka kamar yadda Dokar Zabe take da shi, kuma hukumar INEC ta yi aiki ne cikin ikon da doka ta ba ta.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa dukkan wa'adin da aka sanya a cikin jadawalin zaben 2027 ya yi daidai da tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.

INEC ta kalubalanci hukuncin farko

A cikin takardar daukaka karar da ta shigar ranar 25 ga watan Mayu, INEC ta gabatar da dalilai tara da ta bukaci kotun ta yi la'akari da su tare da soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya.

Hukumar ta ce karar da jam'iyyar Youth Party (YP) ta shigar ba ta da amfani a aikace, domin ta dogara ne kan hasashe kawai.

Kara karanta wannan

Hukumar NCAA ta hukunta matukin jirgin sama da ya sauka a titin motoci a Najeriya

Ta kuma yi zargin cewa kotun farko ta hana ta damar samun adalci saboda rashin yanke hukunci kan wasu muhimman batutuwan shari'a da ta gabatar, in ji rahoton Punch.

Kotun farko ta dora laifi kan INEC

Tun farko, Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukuncin cewa INEC ba ta da ikon takaita wa'adin da Dokar Zabe ta tanada ga jam'iyyun siyasa wajen gudanar da zabukan fidda gwani da gabatar da sunayen 'yan takara.

Kotun ta kuma soke wa'adin ranar 10 ga watan Mayu da INEC ta sanya wa jam'iyyu domin gabatar da rajistar mambobinsu da bayanan 'yan takara.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman shari'a a kotunan Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai da sabon hukuncin Kotun daukaka kara, an soke dukkan wadannan umarni, lamarin da ya bai wa INEC damar ci gaba da amfani da jadawalin zaben 2027 da ta fitar.

INEC ta nemi karin kudi kafin 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya mika bukatarsa ga hukumar RMAFC mai kula da rarraba kudade.

Amupitan ya buƙaci hukumar RMAFC ta amince da ƙarin kuɗaɗe tare da tabbatar da an tallafa wa INEC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

A cewarsa, kuɗin gudanar da zaɓen gwamna guda ɗaya yanzu ya zarce jimillar kuɗin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262