ADC Ta Ce Ta Shirya Karbar Gwamna Dauda Lawal na Zamfara daga PDP

ADC Ta Ce Ta Shirya Karbar Gwamna Dauda Lawal na Zamfara daga PDP

  • Jam’iyyar ADC a Zamfara ta ce mutum 100 ne suka sauya sheƙa zuwa tafiyarta cikin kwana 10 da suka wuce
  • Shugaban ADC na jihar, Alhaji Kabiru Garba, ya ce jam’iyyar ta bude kofa ga kowa daga kowace jam’iyyar siyasa
  • Garba ya bayyana cewa ADC za ta karɓi Gwamna Dauda Lawal idan ya yanke shawarar shigowa jam'iyyar daga PDP

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Garba, ya bayyana cewa yana cigaba da karbar masu sauya sheka.

Kabiru Garba ya ce sama da mutum 100 daga jam’iyyu daban-daban ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar cikin kwana 10 da suka gabata.

ADC ta ce za ta iya karbar gwamnan Zamfara
ADC ta ce za ta iya karbar gwamnan Zamfara. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Tribune ta rahoto cewa ya fadi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai da yammacin Juma’a a Gusau, inda ya ce jam’iyyar na karɓar sababbin mambobi a kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sababbin mutane da suka sauya sheƙa suna kara ƙarfafa jam’iyyar, yana mai cewa ADC ta balaga kuma ta shirya fuskantar ƙalubalen siyasa a jihar.

Yadda ADC ke kara karbuwa a jihar Zamfara

Kabiru Garba ya bayyana cewa a kowace rana jam’iyyar na karɓar sababbin mambobi daga jam’iyyu daban-daban a fadin jihar Zamfara.

Daily Post ta wallafa cewa ya shugaban ya ce:

“Tun cikin kwanaki 10 da suka wuce, fiye da mutum 100 ne suka fice daga jam’iyyu daban-daban suka koma ADC.
"Wannan yana nuna yadda mutane ke samun kwarin gwiwa da yarda da jam’iyyar,”

Ya ce karɓar sababbin mutane daga kowace jam’iyya alama ce cewa ADC na da karbuwa kuma mutane na ganin amfanin sauya sheƙa zuwa gare ta.

ADC ta ce a shirye take ta karɓi Dauda Lawal

A yayin ganawar, Kabiru Garba ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ADC a shirye take ta karɓi Gwamna Dauda Lawal idan har ya yanke shawarar sauya sheƙa.

Kabiru Garba ya ce:

“Jam’iyyarmu ba ta keɓance kowa ba. Idan har Gwamna Dauda Lawal ya ga dacewar sauya sheƙa zuwa ADC, to za mu tarbe shi hannu bibbiyu,”

Jam’iyyar ADC dai na daga cikin jam’iyyun da ke kokarin kara ƙarfi a matakin jiha da na ƙasa, musamman bayan hadakar da 'yan adawa suka yi a makon da wuce a Abuja.

Sababbin jagororin ADC yayin taro a Abuja
Sababbin jagororin ADC yayin taro a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

An tarbi sakataren ADC a jihar Legas

A wani rahoton, kun ji cewa sabon sakataren rikon kwarya na jam'iyyar ADC, Rauf Aregbesola ya dura jihar Legas a yammacin Juma'a bayan fara aiki da ya yi.

Rahotanni sun nuna cewa tarin magoya bayan jam'iyyar ADC ne suka karbi tsohon gwamnan a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke jihar Legas.

Legit Hausa ta wallafa cewa Rauf Aregbesola ya bukaci 'yan jam'iyyar ADC da su mayar da hankali kan tallata tafiyarsu ba tare da zagi ko cin mutunci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng