"Ni Ke Ɗaukar Nauyin ADC," Haɗakar Atiku, Obi da Sauran Ƴan Adawa na Fuskantar Rugujewa

"Ni Ke Ɗaukar Nauyin ADC," Haɗakar Atiku, Obi da Sauran Ƴan Adawa na Fuskantar Rugujewa

  • Jam'iyyar ADC na ci gaba da fuskantar matsala tun bayan haɗewa da jagororin adawar Najeriya da ke shirin kalubalantar Tinubu a 2027
  • Ɗan majalisa wakilai ɗaya na ADC, Hon. Leke Abejide ya bayyana cewa babu inda wannan haɗaka za ta je domin ba za su iya ja da APC ba
  • Ya yi barazanar cewa zai iya barin ADC zuwa APC a duk lokacin da ya ga dama domin yana da ƴancin yin hakan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya ɗaya tilo da jam'iyyar ADC ke da shi, Hon. Leke Abejide ya ce haɗakar ƴan adawa a jam'iyyarsa ba za ta kai ga nasara ba.

Hon. Abejide ya yi ikirarin cewa shi ne mai ɗaukar nauyin ADC, kuma zai iya sauya sheƙa zuwa APC a duk lokacin da ya ga dama saboda yana da ƴancin haka.

Dan Majalisar Yagza daga jihar Kogi, Leke Abejide.
Dan Majalisar ya yi hashashen rugujewar haɗakar yan adawa a ADC Hoto: Abraham Ibukun
Asali: Facebook

Ɗan Majalisar ya faɗi haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv a cikin shirin Sunrise Daily ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC na fuskantar matsala daga ƴaƴanta

Abejide wanda ke wakiltar mazaɓar Yagba ta Jihar Kogi, ya bayyana kansa a matsayin fuska kuma mai ɗaukar nauyin jam’iyyar ADC a Najeriya, inji The Cable.

A ranar Laraba, manyan 'yan adawa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar suka ayyana ADC a matsayin jam'iyyar da za su ƙalubalanci APC a 2027.

Sai dai ɗan majalisar ya bayyana shakku kan wannan ƙawance, ya ce bai ga alamar nasara a tattare da ƴan PDP, LP da ma jam’iyyar APC da suka koma ADC ba.

“Na shiga wannan jam’iyya tun 2018, kuma ni ne fuskar ADC a Najeriya. Gaskiya za a iya cewa ADC na wanzuwa ne kawai a Jihar Kogi,” in ji shi.

Ɗan Majalisar ADC ya nesanta kansa daga haɗaka

Abejide ya nesanta kansa daga ƙungiyar haɗakar da ake kokarin kafa wa, inda ya ce ya ki halartar duk wata ganawa da ta shafi ƙawancen duk da Ralph Nwosu, tsohon shugaban ADC, ya nemi ya zo.

“Mutanen da ban taɓa tsammanin za su shiga ADC ba su ke shiga yanzu. Ni kam ban ga abin muke da shi iri ɗaya ba, mutanen da muke da dabi’u da manufofi ɗaya yawanci suna cikin APC.
"Ni ne mai ɗaukar nauyin ADC. Shugaban jam’iyya na ƙasa ya yi magana da ni, amma ban halarci ko ɗaya daga cikin taronsu ba. Sun yi duk abin da za su yi, amma ban halarta ba.

- Hon. Leke Abejide.

Yan adawa sun haɗe a ADC.
'Ɗan Majalisar Kogi ya yi barazanar fita daga ADC Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Dangane da sauya sheƙar ƴan adawa zuwa ADC kuwa, ɗan Majalisar ya ce:

“Kamar yadda Shugaba Tinubu ya ce, kowa na da ’yanci a Najeriya. Ko gobe na yanke shawarar komawa APC, babu wanda zai hana ni. Saboda haka su ma idan sun yanke shawarar zuwa ADC, wannan hakkinsu ne."

Haɗakar ADC na ƙara fuskantar matsaloli

A wani labarin, kun ji cewa wata kungiya cikin jam’iyyar ADC ta yi fatali da nadin Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyya na rikon ƙwarya.

A cewar ƙungiyar, wannan mataki ya saɓa tanadin dokar kundin tsarin jam'iyyar saboda ba a tuntuɓi INEC ko shugabannin ADC na jihohi ba.

Wannan matsala ta taso ne awanni kaɗan bayan haɗakar ƴan adawa ta rungumi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta tunkari zaɓen 2027 da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262