Atiku Ya Yi wa Tinubu Dariya bayan Trump Ya Ki Gayyatar Shi Taron Shugabannin Afrika
- Atiku Abubakar ya ce ƙin gayyatar Najeriya a taron kasashen Afirka biyar da Donald Trump zai yi wulakanci ne ga Bola Tinubu
- Ya ce rashin gayyatar ba kuskure ba ne, illa hukunci ne mai zafi kan gazawar Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Tinubu
- Atiku ya kuma ce Bola Tinubu ya lalata martabar Najeriya a idon duniya, inda ya jaddada cewa ADC na shirin ceto ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya soki Bola Tinubu bayan Amurka ta fitar da ƙasashen Afirka biyar da za su gana da Donald Trump, ba tare da Najeriya ba.
Atiku, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya bayyana cewa ƙin gayyatar Najeriya ba kuskure ba ne, hukunci ne da ke nuna gazawar gwamnatin Tinubu.

Asali: Facebook
Daily Trust ta rahoto Shaibu ya ce ganawar za ta gudana a ranar 9 ga Yuli, 2025 a fadar White House.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Amurka, Donald Trump zai karɓi shugabannin ƙasashen Gabon, Guinea-Bissau, Liberia, Mauritania da Senegal.
Atiku: 'Da gangan Trump ya cire Najeriya'
A cewar Atiku, Najeriya ce ke da yawan jama'a a Afirka, amma yanzu ta rasa mutunci da darajar da take da ita a baya, kafin jam’iyyar APC ta lalata komai.
Business Day ta wallafa cewa ya ce:
“Tun da Tinubu ya karɓi ragamar ECOWAS, ya ɓata haɗin gwiwa da wasu ƙasashen Yammacin Afirka, wanda hakan ya sa wasu ƙasashe uku suka fice daga kungiyar."
"Najeriya ce ta kasance madogara a harkokin diflomasiyya, amma yanzu ba a ma tunawa da ita. Wani lokaci ma ana kallonta a matsayin matsala."
Atiku: 'Tinubu ya maido Najeriya ‘uwar ɓarna’
Atiku ya ce Najeriya yanzu ta zama wata ƙasa da ba ta da tasiri a idon duniya, kuma haka ya faru ne saboda yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da harkokin ƙasa ba tare da hangen nesa ba.
Ya ce:
“Yayin da wasu ƙasashen ke tsara tsarin kasuwanci da Amurka, mutanen gwamnatin Tinubu na shakatawa a St. Lucia, yayin da tattalin arzikin ƙasa ke tabarɓarewa.”
Ya kuma karyata rahotannin da ke cewa Gilbert Chagoury, wanda ake dangantawa da Trump, yana da tasiri a gwamnati.
A cewarsa:
“Chagoury ba abokin Trump ba ne. Shi dai babban mai bayar da gudunmawa ne ga gidauniyar Clinton.”
Atiku ya bayyana cewa kawancen da jam’iyyar ADC ke jagoranta shi ne mafita ga Najeriya. Ya ce ana bukatar ceto kasar daga “berayen birni” da suka mamaye gwamnati a yanzu.

Asali: Facebook
Ya kammala da cewa bayan zama abin kunya, lamarin ya jawo wulakanta Najeriya gaba ɗaya a idon duniya.
Tinubu ya ce ya samu Najeriya a rikice
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ya samu Najeriya a birkice a lokacin da ya hau mulki.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne yayin wani taro na musamman da ya yi da 'yan Najeriya mazauna kasar Sait Lucia.
Sai dai duk da haka, Bola Tinubu ya ce ya dauki matakan da suka fara farfado da tattalin arzikin kasar bayan zuwansa.
Asali: Legit.ng