Ana Neman Rusa Takarar Atiku, INEC Ta Yi Magana kan Sunayen 'Yan Takara na Tsagin ADC

Ana Neman Rusa Takarar Atiku, INEC Ta Yi Magana kan Sunayen 'Yan Takara na Tsagin ADC

  • Hukumar zaben Najeriya (INEC) ta musanta ikirarin cewa shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala ya samu damar shigar da bayanan 'yan takara
  • Shafin INEC ya nuna Sanata David Mark ne halastaccen shugaban ADC na ƙasa, yayin da Rauf Aregbesola ke a matsayin sakatare
  • Rikicin shugabanci a jam'iyyar adawa ta ADC na ci gaba da ƙara kamari gabanin babban zaɓen 2027 da ke tafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙaryata ikirarin cewa ta bai wa tsagin ADC karkashin jagorancin Nafi'u Bala damar tura sunayen 'yan takara gabanin zaben 2027.

Hukumar INEC ta musanta lamarin, tana mai cewa ba ta bai wa tsagin Nafi'u Bala lambar shiga shafin tura bayanan 'yan takarar jam'iyyar ADC ba.

Hukumar INEC.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan yayin ganawa da jami'an zabe a Abuja Hoto: INEC Nigeria
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani rahoto da ya bazu kafafen sada zumunta, ya yi ikirarin cewa ɓangaren Nafiu Bala ya kammala loda sunayen 'yan takara a shafin INEC da ake amfani da shi wajen karɓar sunayen 'yan takara.

Kara karanta wannan

"Tinubu zai sha kaye," An yi hasashen gwamnan da zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Hukumar INEC ta ƙaryata ikirarin

Da aka tuntubi Daraktar Wayar da Kan Masu Zaɓe da Hulɗa da Jama'a ta INEC, Misis Victoria Eta-Messi, ta bayyana cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne.

Ta jaddada cewa hukumar INEC ba ta amince da Nafiu Bala a matsayin shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A amssr da ta bayar a takaice, jami'ar INEC ta ce rahoton bai wa Nafi'u Bala lambar shiga shafin tura bayanan yan takara, "ba gaskiya ba ne."

Shafin INEC ya nuna David Mark

Binciken da aka gudanar a shafin hukumar INEC da ke ɗauke da bayanan jam'iyyun siyasa ya nuna cewa har yanzu Sanata David Mark ne aka bayyana a matsayin shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa.

Haka kuma, shafin ya nuna Ogbeni Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa, wanda ke nuna cewa su ne jami'an jam'iyyar da INEC ta amince da su wajen gudanar da harkokin doka, ciki har da miƙa sunayen 'yan takara.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya kawo hujjoji, ya zargi Tinubu da naɗa wanda zai ruguza 'yan adawa a INEC

Rikicin jam'iyyar ADC na ci gaba

Lamarin na zuwa ne yayin da rikicin shugabanci ke ci gaba da dabaibaye jam'iyyar ADC, inda ɓangarori daban-daban ke ikirarin su ne halastattun shugabannin jam'iyyar kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Rikicin ya ƙara ɗaukar sabon salo bayan ikirarin da ɓangaren Nafiu Bala ya yi cewa ya samu damar shiga tsarin INEC tare da loda sunayen 'yan takara, ikirarin da hukumar zaɓen ta musanta gaba ɗaya.

Nafiu Bala.
Shugaban tsagin jam'iyyar ADC na kasa, Nafiu Bala a taron da suka shirya a Abuja Hoto: Nafiu Bala
Source: Facebook

ADC ta dora sunan Atiku a shafin INEC

Tun farko, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta sanya bayanan 'dan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da mataimakinsa, Rotimi Amaechi a shafin INEC.

Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa INEC ta ba su lambar shigar da bayanan yan takara.

ADC ta ce hakan wani muhimmin mataki ne a shirye-shiryenta na tunkarar 2027, tare da jaddada aniyarta ta kawar da Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262