Hisbah Ta Kafa Sabuwar Doka kan Masu Tura Finafinai a Kano

Hisbah Ta Kafa Sabuwar Doka kan Masu Tura Finafinai a Kano

  • Hukumar Hisbah ta sanar da haramta sana'ar sauke da rarraba fina-finai ta wayoyin salula a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar
  • Hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda zargin wasu masu sana'ar da yada bidiyoyin batsa wanda ya saba da Musulunci
  • Hisbah ta gargadi masu karya dokar cewa za a dauki matakin shari'a a kansu, tare da bukatar su koma wasu halastaccen aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar Hisbah ta Kano ta sanar da haramta sana'ar sauke da rarraba fina-finai ta amfani da wayoyin salula a fadin jihar.

Hukumar ta bayyana cewa matakin wani bangare ne na kokarinta na kare tarbiyyar al'umma da kuma inganta koyarwar addinin Musulunci a jihar.

Hukumar Hisbah ta waiwayi masu tura fina-finai a Kano
Shugaban hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Ibrahim Daurawa Hoto: Sheikh Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta shafi dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin rage yaduwar badala.

Kara karanta wannan

Amurka ta kara taso Najeriya a gaba game da kare rayukan kiristoci

Hisabah ta sa doka a Kano

Daily Post ta wallafa cewa Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya bayyana cewa ba za a lamunci raba ci gaba da raba fina-finai na.

A cewar Dakta Aminuddeen, hukumar ta dauki wannan mataki ne bayan samun korafe-korafen cewa wasu masu gudanar da sana'ar na yada fina-finan batsa.

Hisbah za ta hukunta masu tura fim
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yamma Hoto: Legit.ng
Source: Original

Haka kuma suna yaɗa bidiyoyi da ake ganin sun saba wa koyarwar Musulunci da kuma al'adun mutanen Kano.

Ya ce hukumar ta tura jami'anta domin sa ido kan yadda ake bin wannan umarni ta hanyar sintiri da kuma ayyukan tabbatar da doka a sassa daban-daban na jihar.

Hisbah ta fara da ido a Kano

Ya kara da cewa duk wanda aka samu yana karya wannan umarni zai fuskanci hukunci bisa tanadin dokokin Jihar Kano.

Hukumar ta shawarci wadanda wannan matakin ya shafa da su nemi wasu halastattun hanyoyin samun abin rayuwa maimakon ci gaba da gudanar da sana'ar da aka dakatar.

Kara karanta wannan

'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya

A cewar Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, karuwar lalacewar tarbiyya a tsakanin matasa na da alaka da kallon fina-finai da bidiyoyin da ba su dace ba.

Ya ce manufar wannan mataki ita ce kare matasa daga abubuwan da ka iya gurbata tarbiyyarsu tare da kiyaye kyawawan dabi'u da al'adun al'umma.

Auren gata Hisbah ta kafa sharadin saki

A baya, kun samu labarin cewa shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano ya gargadi ma’auratan da za su shiga shirin auren gata na jihar game da saki ba tare da izini ba yayin da ke kokarin rage mutuwar aure.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa ba za a ba su damar yin saki ba tare da sun fara kai rahoto ga Hisbah domin sasanci da kuma kokarin warware matsalar da za ta iya jawo rabuwar auren ba.

Ya yi wannan gargadin ne yayin wata ziyara da ya kai inda ake gudanar da gwajin lafiya ga masu shirin aure a ranar Laraba, 10 ga Mayun 2026 a kokarin da gwamnatin jihar Kano ke yi na ingana rayuwar ma'auratan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng