Atiku ko Obi?: Malamin Addini Ya Hango Wanda Jam'iyyar ADC Za Ta ba Tikiti a 2027

Atiku ko Obi?: Malamin Addini Ya Hango Wanda Jam'iyyar ADC Za Ta ba Tikiti a 2027

  • Malamin addinin Kirista, Primate Ayodele ya ce Atiku Abubakar ne zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a 2027, ba Peter Obi ba
  • Ya gargadi APC cewa za ta iya faduwa zaɓe idan shugabanninta suka bijirewa maganganunsa, inda ya nuna damuwa kan makomar jam'iyyar
  • A hannu daya kuma Festus Keyamo ya zargi ƙungiyar haɗakarsu Atiku da cewa tana ƙoƙarin amfani da Peter Obi don samun ƙuri'u a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Shugaban Cocin INRI Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen wanda jam'iyyar haɗakar 'yan adawa ta ADC za ta zaɓa a matsayin ɗan takararta a zaɓen 2027.

Primate Ayodele ya ce ya hango cewa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ne zai samu tikitin takarar shugaban kasa a ADC, ba Peter Obi ko Nasir El-Rufai ba.

Primate Elijah Ayodele ya ce Atiku Abubakar zai samu tikitin takara a 2027 a karkashin ADC
Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi sun kaddamar da jam'iyyar hadaka ta ADC. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Hasashen Ayodele game da ADC da APC a 2027

Babban faston da ke da zama a Legas ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayodele ya kawar da yiwuwar zaɓen daya daga cikinsu Rotimi Amaechi, Peter Obi ko Nasir El-Rufai a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027.

Malamin addinin, ya bayyana cewa:

“'Yan kungiyar hadakar adawa za su zaɓi Atiku. Atiku ne ɗan takararsu, ba El-Rufai ba, ba Amaechi ba ko wani daban ba. Amma akwai wani sharadi.”

Primate Ayodele ya ƙara da cewa:

“Babu wani tabbaci na cewa jam’iyya mai mulki (APC) za ta iya cin zaɓe a 2027. Idan suka bijirewa maganganu na, to lallai za su fadi zaben."

Kalli bidiyon a kasa:

Peter Obi ya mika bukata ga kungiyar hadaka

Wannan yana zuwa ne 'yan kwanaki bayan da muka ruwaito cewa Peter Obi ya miƙa bukatarsa ga kungiyar hadaka ta yin wa'adi daya rak idan aka ba shi dama.

Jagoran kungiyar Obidient na kasa, Dr. Yunusa Tanko, jim kadan bayan an yi wa Obi nadin sarautar 'Sarkin Maskan' a masarautar Pantami, jihar Gombe.

A cewar Tanko, tsohon gwamnan jihar Anambra baya buƙatar fiye da shekaru huɗu don sauya ƙasar da kuma ceto tattalin arzikinta daga rugujewa.

Festus Keyamo ya yi zargin cewa su Atiku za su yaudari Peter Obi ne kawai a 2027, ba za su ba shi tikiti a ADC ba
Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai sun ayyana ADC matsayin jam'iyyar hadaka. Hoto: Hoto: @muhammaddayyiib
Asali: Twitter

'Atiku zai yi amfani da Obi ne kawai' - Keyamo

Amma kuma, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi zargin cewa ƙungiyar haɗaka da aka kafa don hamɓarar da Shugaba Bola Tinubu a 2027 tana ƙoƙarin amfani da Peter Obi ne kawai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Festus Keyamo yana cewa:

“Kaddamar da jam'iyyar ADC ya rushe duk wani shiri na PDP, dukkanin jiga-jiganta ne a hadakar, kuma an san PDP ce jam'iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya.
“A bayyana yake cewa hadakar 'yan adawa an gina ta ne karkashin mabiyan Atiku na PDP, wanda shi kuma yake neman tikitin takara a 2027 ruwa a jallo, bai da wani buri bayan haka.

“Mutumin da wadannan tsofaffin suke son yi wa wayau, ko in ce suke son yaudararsa shi ne Peter Obi. Suna son ya ba su ƙuri’unsa ne kawai, amma ba sa so su taba ba shi tikitin shugaban ƙasa ba.”

Atiku, El-Rufai, Obi sun zabi jam'iyyar ADC

Tun da fari, mun ruwaito cewa, kungiyar haɗakar jam’iyyun adawa ƙarƙashin Atiku Abubakar ta zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta fuskanci APC a zaɓen 2027.

An naɗa David Mark a matsayin shugaban rikon ƙwarya na jam’iyyar, Rauf Aregbesola a matsayin sakatare, yayin da Bolaji Abdullahi zai riƙe muƙamin kakaki.

Shugabannin adawa irinsu Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai sun bayyana kwarin gwiwa cewa ADC za ta iya doke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.