Mutanen da za Su Iya Neman Takarar Shugaban Kasa a karkashin Hadakar ADC
Yayin da siyasar 2027 ke kara zafi, wasu fitattun siyasa da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar sun karɓe iko da jam’iyyar ADC.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Rahotanni sun nuna cewa wannan hadin gwiwa na adawa na da nufin fitar da dan takara guda daya domin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Asali: Facebook
Legit Hausa ta tattara jerin wasu daga cikin manyan yan adawa da ake hasashen za su nemi tikitin shugaban kasa a karkashin ADC a zabe mai zuwa:
1. Atiku na iya neman takarar shugaban kasa
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takara a zabe da dama da suka gabata, Atiku Abubakar, na daga cikin wadanda ake ganin za su sake fafatawa a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta ruwaito a watan Mayu, 2025, Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai sani ba ko zai sake neman kujerar shugaban kasar, duk da fafutukar samar da hadakar adawa.

Asali: Facebook
Ko da yake har yanzu bai bayyana niyyarsa a fili, rawar da yake takawa a sabon hadin gwiwar ADC na nuna cewa yana shirye-shiryen komawa takarar shugaban kasa.
2. Babu mamaki Peter Obi zai nemi takara
Peter Obi, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar LP a zaben 2023, ya riga ya tabbatar da cewa zai sake tsaya wa takarar shugaban kasa a 2027.
Punch Newa ta ruwaito cewa a wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Ibrahim Umar, Obi ya ce ba zai yi tikitin hadaka da Atiku Abubakar ba.

Asali: Twitter
Obi, Wanda tsohon gwamnan Anambra ne kuma mai zazzafar suka ga gwamnatin Bola Tinubu, ya bayyana cewa idan ya ci zabe, zai yi shekara hudu kacal babu haɗama.
3. Amaechi na iya neman kujerar Tinubu
Tsohon ministan sufurin jiragen kasa kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, yana daga cikin wadanda suka shiga sabon tafiyar ADC.
Ana kallon Amaechi a matsayin fitaccen dan siyasa daga Kudu maso Kudu wanda zai iya ba jam’iyyar APC kalubale mai tsanani idan har ya samu tikiti.
A hira da yayi a kwanakin baya, Daily Trust ta ruwaito Amaechi na bayyana cewa akwai yiwuwar ya tsaya takara, amma lokaci ne kawai zai tantance hakan.
Amaechi ya nemi tikitin APC amma ya zo bayan Bola Tinubu a zaben tsaida gwani a 2022.
4. Nasir El-Rufa'i zai yi takara a ADC?
Tun bayan samun sabani da tsohuwar gwamnatinsu ta APC, Nasir El-Rufa'i ke caccakar salon mulkin Bola Ahmed Tinubu.
Ya sha zargin cewa APC ta sauka daga layin da aka kafa ta a kai na ceto talaka daga kangin wahala da ake fama da ita a fadin Najeriya.

Asali: Twitter
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda aka san shi da murdadden salon siyasa, na cikin jiga-jigan da suka hade a ADC.
Ko da yake bai fito fili da wata sanarwa ba, akwai hasashen cewa zai iya tsayawa takara ko kuma zama daya daga cikin masu zabar dan takara da zai kara da APC.
Tun gabanin zaben 2007, a lokacin yana minista ake ta rade-radin El-Rufai zai nemi takarar shugaban kasa, a karshe aka tsaida gwamna Umaru Yar'Adua.
5. Tambuwal ya taba harin takarar shugaban kasa
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya taba janyewa a zaben fidda gwani na PDP a 2022 don bai wa Atiku Abubakar dama.
Duk da cewa yana yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Kudu a yanzu, ana ganin Tambuwal na iya komawa takarar shugaban kasa idan yanayin siyasa ya sauya.
Yana dada cikin manyan PDP da suka amince da dunkulewa a hadakar adawa, duk da bai bayyana rabuwa da PDP ba a halin yanzu.
6. Tsohon dan takara, Dele Momodu
Fitaccen dan jarida kuma dan takarar shugaban kasa a PDP a baya, Dele Momodu, bai bayyana niyyarsa a kan batun takara ba tukuna.
Amma rawar da yake takawa a cikin sabon hadin gwiwar ADC na nuna cewa bai yi baya-baya da siyasa gaba.

Asali: Facebook
Dele Momodu ya bayyana cewa hadin gwiwar adawar na ADC sakamakon shirin da ya dauki watanni 18 ana yi a asirce.
Ya ce ko da yake babu wani karba-karba da aka tsara yanzu, sun amince kada su bari siyasa ta raba kawunansu.
7. Tsohon dan takarar ADC, Dumebi Kachikwu
Duk da har yanzu a fusace ya ke, kuma a cikin jam'iyyar aka same shi, dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2023, Dumebi Kachikwu, na iya neman takara.
Bayan shigowar yan adawa zuwa ADC, ya bayyana sabon hadin gwiwar da aka yi da jam’iyyarsa a matsayin abin da ya saba da doka ba.

Asali: Twitter
Duk da cewa rikicinsa da sababbin shugabannin na iya hana shi samun tikitin jam’iyyar, ana sa ran zai ci gaba da adawa da sababbin 'yan jam'iyyar har zuwa wani lokaci.
Tsohon dan takara a ADC zai jawo rikici
A baya, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaben 2023, Dumebi Kachikwu, ya bayyana rashin amincewarsa da sabuwar haɗakar adawa.
Ya ce jiga-jigan yan siyasa da suka kunno kai zuwa cikin jamiyyarsu, sun biyo ta haramtacciyar hanya, domin ba Ralph Nwosu ne shugaban ADC a yanzu ba.
A cewarsa, sabon tsarin da aka ƙaddamar a ranar Laraba ba halastacce ba ne, domin an yi amfani da shugabannin bogi wadanda wa'adinsu ya kare tun a shekarar 2022.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng