Shiga ADC: Ministan Buhari, Hadi Sirika Ya Karyata Wike da Fadar Shugaban Kasa
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce bai shiga kawancen jam’iyyar ADC da ‘yan adawa ke yi domin kifar da Bola Tinubu a 2027 ba
- Rahotanni sun nuna cewa Hadi Sirika ya bayyana cewa yana nuna cikakken goyon baya ga jam’iyyar APC da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Sirika ya caccaki ministan Abuja, Nyesom Wike da hadimin Tinubu, Bayo Onanuga bisa yada labarin shigarsa ADC ba tare da tantance gaskiyarsa ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika, ya musanta rahotannin da ke cewa ya shiga kawancen jam’iyyar ADC.
'Yan adawan Najeriya sun fara amfani da jam'iyyar ADC ne domin fuskantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Hadi Sirika ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a X, yana mai caccakar wasu manyan jami’ai da suka hada da ministan birnin tarayya, Nyesom Wike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga Nyesom Wike, tsohon ministan ya caccaki da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga bisa cewa ya koma ADC.
“Ina APC, ban shiga ADC ba,” Sirika
Bayan karyata rade radin, Hadi Sirika ya ce har yanzu yana nan daram da jam’iyyar APC kuma bai da niyyar barinta.
The Cable ta wallafa cewa Hadi Sirika ya ce:
“Na kalli Nyesom Wike a Arise TV yana ikirarin cewa na shiga kawancen 'yan adawa.
"Cikin mamaki sai na sake karanta wani rahoto a Premium Times da aka danganta da Bayo Onanuga da yake yin wannan da’awa.”
Hadi Sirika ya ce yana daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC tun farko, kuma shi ne ya ba jam’iyyar sunan da take amfani da shi yanzu.
Ya kara da cewa:
“Ina nan a cikin APC. Ba ni da wata niyyar barin jam’iyyar. Zan ci gaba da kasancewa a inda Shugaba Buhari yake. Idan za ku ƙi shi, to ku ƙi ni, ni ma,”
Hadi Sirika ya caccaki Wike da Onanuga
Sirika ya bayyana cewa matakin da Wike da Onanuga suka dauka bai dace ba, domin kamata ya yi su tabbatar da gaskiyar labari kafin su wallafa shi.
A cewar shi:
“A irin matsayinsu, ya kamata su rika bincika gaskiyar kowanne labari kafin su yada shi.
"Na bukaci mambobin jam’iyyar mu da su yi watsi da wadannan maganganu kuma kada su damu da su,”
Tsohon ministan ya ce yana da kyakkyawan ra’ayi kan jam’iyyar APC da kuma shugabancinta, kuma yana fatan mutane za su ci gaba da ba da goyon baya ga jagorancin jam’iyyar.
A ranar Laraba ne aka gudanar da bikin kaddamar da ADC a matsayin dandalin kawancen ‘yan adawa a Abuja.
Fadar shugaban kasa ta caccaki ADC
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi wa 'yan siyasa martani kan shiga ADC domin kifar da Bola Tinubu a 2027.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce kiyayya ga Bola Tinubu ne ya sanya 'yan siyasar haduwa a ADC.
Bayo Onanuga ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da masu hadaka a ADC domin a cewar shi, ba su da wata manufa mai kyau.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng