Atiku ko Obi: Sule Lamiɗo Ya Fito da Abin da ke Ransa, Ya Faɗi Wanda Zai Marawa Baya a 2027

Atiku ko Obi: Sule Lamiɗo Ya Fito da Abin da ke Ransa, Ya Faɗi Wanda Zai Marawa Baya a 2027

  • Sule Lamido ya bayyana cewa zai marawa Peter Obi baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 matukar jam'iyyar haɗaka ta tsayar da shi
  • Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya ce a shirye yake ya goyi bayan duk wanda ADC ta ba takara domin kawo karshen mulkin jam'iyyar APC
  • Obi, tsohon ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP ya yi alƙawarin cewa shekaru huɗu kaɗai zai yi idan ya karɓi mulki a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa a shirye yake ya goyi bayan Mista Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sule Lamido ya ce matukar jam'iyyar haɗaka watau ADC ta tsayar da Peter Obi takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa, zai mara masa baya da duka ƙarfinsa.

Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.
Sule Lamido ya ce a shirye yake ya marawa Peter Obi baya a zaɓen 2027 Hoto: Sule Lamido
Asali: Twitter

2027: Peter Obi na kara samun goyon baya

Hakan ya yi daidai da matsayar ƙungiyar ƴan Arewa ta Tsakiya a Najeriya da ta ce babu wata dama da ta fi ganin ta dace face a mara wa Peter Obi baya, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar kungiyar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023 yana da kyakkyawan tarihi na cika alkawari kuma yana da nagarta, kamar yadda Punch ta kawo.

Da yake tsokaci kan haka, Sule Lamido, ya ce ba shi da damuwa idan ADC ta ba Obi tikitin takarar shugaban ƙasa, zai fito ya mara masa baya ba tare da ya bar PDP ba.

Wane ɗan takara Sule Lamido zai goyi baya?

Da aka tambaye shi kan yiwuwar goyon bayan Obi wanda ya sha alwashin yin zango guda (shekara huɗu) kacal idan ya lashe zaɓen 2027, tsohon gwamnan ya ce:

“Idan haɗakar jam’iyyun adawa ta zaɓi Peter Obi ko wani mutum daban da ke da niyyar ceto Najeriya, zan mara masa baya, amma ina nan a PDP, ya kamata mu wuce batun ƙabilanci da yanki.”

"Shi shugabanci ya kamata ya ta’allaka ne kan cancanta da hangen nesa, ba wurin da mutum ya fito ba. Wane amfana Arewa ta yi da samar da mafi yawan shugabannin ƙasa? Har yanzu yankin yana fuskantar koma baya.
"A shirye nake na bi kowanne tsari da zai iya ƙalubalantar jam’iyyar APC da ceto Najeriya. Zan goyi bayan duk wanda ke da wannan manufa.”
Sule Lamido tare da Peter Obi.
Sule.Lamido ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta daina duba yanki ko kabilanci wajen zaɓen shugaba Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya kuma ƙara cewa tsarin karɓa-karɓa tsakanin Arewa da Kudu wata dabara ce da jam’iyyar PDP ta ƙirƙiro domin magance matsalar da ta biyo bayan soke zaɓen 12 ga Yuni.

Sule Lamido ya dura kan ministan Abuja, Wike

A wani labarin, kun ji cewa Sule Lamido ya bayyana damuwarsa matuƙa kan yadda ministan Abuja, Nyesom Wike ke ƙoƙarin maida PDP kadararsa ta kai da kai.

Tsohon gwamnan ya ce yana maraba kuma zai karbi duk wata haɗaka hannu bibbiyu, matuƙar za ta kalubalanci Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Sule Lamido, ya bayyana takaicin yadda jam'iyyarsa zuba idanu a kan wasu tsirarun ’yan jam’iyya suna aikata abin da suka ga dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262