Amurka Ta Sake Karfafa Saudiyya Ana tsaka da Yaki da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
- Amurka ta amince da sayar wa Saudiyya makamai da kayan kariyar sama na dala biliyoyin dala domin ƙarfafa tsaronta
- Makaman sun haɗa da 'Advanced Precision Kill Weapon Systems' har guda 20,000, yayin da kamfanin BAE zai jagoranci aiwatar da yarjejeniyar sayarwar
- Matakin ya zo ne yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta, bayan harin makamai masu linzami da Houthi suka kai filin jirgin Abha a Saudiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Riyadh, Saudi Arabia - Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar a ranar Laraba cewa ta amince da sayar wa Saudiyya makamai da kayan kariyar sama.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa darajar makaman ta kai kusan dala biliyan 1.96 domin inganta tsaronta.

Source: Getty Images
Musabbabin kulla yarjejeniyar Amurka da Saudiyya
Rahoton Anadolu ya ce wannan mataki na da nufin ƙarfafa tsaron Saudiyya yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ƙamari.

Kara karanta wannan
Mary Habila: Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar budurwa a gidan Ministan Tinubu
Ma'aikatar ta bayyana cewa wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen cimma manufofin harkokin wajen Amurka da tsaron ƙasarta.
Ta ce ƙarfafa tsaron Saudiyya, wacce babbar ƙawar Amurka ce ba mamba a NATO ba, zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a yankin Tekun Fasha.
Daga cikin makaman da Saudiyya ke neman saya akwai na'urorin Advanced Precision Kill Weapon Systems har guda 20,000 tare da warheads ɗinsu.
Rundunar sojin ruwan Amurka ta bayyana cewa waɗannan makamai suna ba da damar lalata wuraren hari cikin daidaito tare da rage barna ga fararen hula.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce kamfanin BAE Systems da ke Nashua, jihar New Jersey, shi ne zai kasance babban kamfanin da zai aiwatar da wannan yarjejeniyar sayar da makamai.

Source: Getty Images
Muhimmancin makaman ga kasar Saudiyya
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan sayayya za ta inganta ƙarfin Saudiyya wajen dakile barazanar da ake fuskanta a yanzu da kuma waɗanda ka iya tasowa nan gaba.
Haka kuma za ta ƙarfafa haɗin kai da daidaiton aiki tsakanin dakarun Saudiyya, na Amurka da sauran ƙawayen yankin da na NATO.

Kara karanta wannan
Babban jigon APC a Arewa ya yi magana kan barin jam'iyyar bayan Tinubu ya zabi Shettima
Wannan mataki ya zo ne yayin da ake ganin Saudiyya na dab da sake shiga sabon rikici da mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran a Yemen.
A ranar Litinin, Houthi sun harba makamai masu linzami zuwa filin jirgin saman Abha da ke kudancin Saudiyya, cewar Times of Israel.
An kai harin ne bayan gwamnatin Yemen ta kai hari filin jirgin saman Sanaa domin karkatar da jirgin da ke ɗauke da tawagar Houthi da ke dawowa daga jana'izar jagoran addinin Iran.
A ƙarshe, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta tabbatar da cewa wannan yarjejeniyar sayar da makamai ba za ta yi wani tasiri mara kyau ga shirin ko ƙarfin rundunar tsaron Amurka ba.
Saudiyya ta nemi alfarmar Trump
An ji cewa Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana yakin Iran a matsayin wata babbar dama ta sauya siyasar yankin Gabas ta Tsakiya gaba daya.
Saudiyya ta karyata zargin ingiza Amurka zuwa yaki, inda tace babban burinta shine kare jama'arta daga hare-haren jiragen mara matuka.
Donald Trump ya ce ana tattaunawa mai kyau da Iran, amma mahukuntan Tehran sun karyata batun tattaunawar yayin da ake fafatawa.
Asali: Legit.ng