Mutane Sun Yi Wa Ɗan Majalisa Rubdugu da Ya Kwatanta Haɗarin Jirgin 2006 da Haɗakar ADC
- Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya, Hon. Clement Jimbo daga jihar Akwa Ibom ya fara shan suka daga ƴan Najeriya kan haɗakar ADC
- Jimbo ya kwatanta haɗakar da ƴan dawa suka ƙulla a ADC da mummunan hatsarin jirgin ADC Airline da ya faru a 2006, hakan ya harzuƙa jama'a
- Mutane sun maida masa martani mai zafi kan wannan kalamai da ya yi, suna cewa bai kamata ya taɓo abubuwan da aka rasa rayuka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hon. Clement Jimbo, wanda ke wakiltar mazaɓar Abak/Etim Ekpo/Ika a Majalisar Wakilai daga jihar Akwa Ibom ya fara shan suka daga ƴan Najeriya.
Ƴan Najeriya sun yi wa ɗan Majalisar rubdugun martani ne bayan ya kwatanta haɗarin jirgin sama na ADC da ya faru a 2006 da jam'iyyar haɗaka ta ADC.

Asali: Twitter
Hon Jombo ya yi wannan kwatance ne a lokacin da yake sukar haɗakar ADC a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba, Legit Hausa ta kawo maku rahoton yadda jagororin adawa suka kulla haɗaka da ADC domin kalubalantar shugaban ƙasa, Bola Tinubu a 2027.
Wane hatsarin jirgi aka yi a Najeriya a 2006?
A shekarar 2006, jirgin saman kamfanin ADC Airline, mai lamba 053 — Boeing 737-200 ya yi hatsari jim kaɗan bayan ya tashi daga filin jirgin saman Abuja.
Wannan hatsari ya girgiza Najeriya, inda mutane 96 daga cikin fasinjoji 105 da ke cikin jirgin saman suka rasa rayukansu.
Har yanzu akwai ‘yan Najeriya da dama da idan suka tuna hatsarin su kan shiga yanayin baƙin ciki, musamman waɗanda suka rasa ƴan uwansu.
Ɗan Majalisa ya kwatanta hatsarin da haɗaka
Ɗan Majalisar ya yi amfani da wannan haɗari a matsayin misali, yana cewa jam’iyyar adawa ta ADC da aka kafa zata gamu da irin wannan kaddara.
“Nawa daga cikinku ne suka tuna jirgin ADC Flight 53 da ya yi hatsari a 2006? Ga shi ya dawo don ya sake yin hatsari. Don Allah kada ku hau!” in ji shi.
Wannan rubutu ya tunzura masu amfani da Facebook, inda sama da mutane 230 suka yi sharhi a ƙasan rubutun, da dama daga cikin su daga jihar Akwa Ibom.

Asali: Facebook
Mutane sun maida wa ɗan Majalisa martani
Wani mai suna, Eno Ekanem
“Ina tuna cewa kawuna na cikin wannan jirgi. Har yau muna cikin baƙin ciki. Idan wannan barkwanci ne, don Allah ka daina."
Ofonime Honesty tambayar ɗan Majalisar ya yi, inda ya ce:
“Shin kana ƙoƙarin tsokanar waɗanda Allah ya karɓi rayuwarsu ne?"
Abasiama Udousoro ya ce:
“Wannan ba daidai ba ne a rika amfani da irin waɗannan abubuwa da suka janyo asarar rayuka wajen yin kwatance."
Wasu da dama sun zargi ɗan majalisar da wulaƙanta waɗanda suka mutu a haɗarin ta hanyar kwatanta su da wata tafiyar siyasa.
George ya soki Atiku da ƴan haɗakar ADC
A wani labarin, kun ji cewa Bode George, ya soki manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP da ke cikin tawagar ƴan haɗaka a ADC.
George ya gargaɗi Atiku Abubakar da wasu 'yan PDP da ke cikin wannan haɗaka ta ADC su zaɓi ɗaya, ko dai su zauna a PDP ko su tafi.
Jigon ya ce haɗakar ADC ba za ta iya zama dandalin adawa kamar PDP ba, domin a cewarsa babu dabarar aiki ko tsari a cikin jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng