Tinubu na kan Siraɗi da Tsohon Shugaban Kwamitin Sulhu na PDP Ya Haɗe da Atiku a ADC

Tinubu na kan Siraɗi da Tsohon Shugaban Kwamitin Sulhu na PDP Ya Haɗe da Atiku a ADC

  • Jam'iyyar PDP ta kama hanyar wargajewa a Gombe da tsohon shugaban kwamitin sulhu, AVM Shehu Adamu Fura ya koma ADC
  • Fitaccen ɗan siyasar, wanda ya taɓa neman tikitin gwamna a inuwar PDP ya ce lokaci ya yi da zai matsa zuwa inda zai kawo ci gaba a ƙasar nan
  • AVM Shehu ya godewa shugabanni da mambobin PDP bisa goyon bayan da suka ba shi na tsawon lokaci, ya masu fatan alheri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Gombe - Tsohon Shugaban Kwamitin Sulhu na Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, Air Vice Marshal (AVM) Shehu Adamu Fura (mai ritaya), ya rungumi haɗakar ADC.

AVM Shehu ya sanar da ficewarsa daga babbar jam'iyyar adawa watau PDP tare da komawa jam'iyyar haɗaka domin kifar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.

PDP ta rasa babban jigo a Gombe.
Tsohon shugaban kwamitin sulhu na PDP ya rikita jam'iyyar, ya koma ADC Hoto: AVM Shehu Adamu Fura
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata wasika da ya aika wa shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Pantami da ke karamar hukumar Gombe, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa AVM Shehu Adamu ya bar PDP?

Tsohon sojan Saman Najeriya ya bayyana cewa matakin da ya dauka ya biyo bayan tattaunawa da nazari mai zurfi da ya yi game da makomarsa a siyasa.

AVM Shehu Adamu ya ce:

"Ina mai sanar da cewa na bar jam’iyyar PDP nan take. Na ɗauki wannan mataki ne bayan zurfin tunani da kuma tattaunawar neman shawari.
"A yanzu kuma na yanke shawarar ci gaba da tafiyar siyasa ta a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, inda nake fatan bada gagarumar gudummawa wajen ci gaban dimokuraɗiyya da kyakkyawan shugabanci don bunƙasa ƙasa.”

AVM Shehu Fura, wanda ya taɓa neman tikitin gwamna a ƙarƙashin PDP a Gombe, ya ce lokaci ya yi da zai raba gari da jam’iyyar da ya yiwa hidima tun daga tushe.

Jigon ya tuna aikin da ya yi a kwamitin sulhu

Ya kuma tunatar da rawar da ya taka a matsayin shugaban kwamitin sulhu na PDP a jihar Gombe, inda ya yi aiki da sauran mambobi wajen ƙarfafa haɗin kai da daidaiton cikin gida na jam’iyyar.

A rahoton Sahara Reporters, AVM Shehu Fura ya ce:

“Ba zan manta da lokacin da na shafe a PDP ba, shi ne lokacin da na yi hidima.
Na samu damar yin aiki a matsayin shugaban kwamitin sulhu na PDP a jihar Gombe, inda muka yi ƙoƙarin haɗa kan ƴan jam’iyya da tabbatar da zaman lafiya a cikin gida.”

AVM Shehu Fuba ya godewa shugabannin PDP

AVM Shehu Fura ya kuma nuna godiyarsa ga shugabannin jam’iyyar PDP da mambobi bisa amincewa da goyon bayan da suka bashi tsawon shekaru.

“Ina godiya ga shugabancin jam’iyyar PDP da mambobi saboda goyon baya da hadin kai da suka bani a tsawon lokaci. Ina yi musu fatan alheri da nasarori a gaba," in ji shi.

ADC ta yi babban kamu a jihar Kano

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takara da ya nemi tikitin gwamnan Kano a inuwar PDP, Ibrahim Ali Amin Little ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

Ibrahim Ali Amin ya bayyana cewa ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda halin da jam’iyyar ke ciki a matakin jiha da na ƙasa.

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ƙara da cewa zai shiga jam'iyyar hadakar adawa watau ADC domin a kara matsa lamba wajen ceto Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262