Fashi da makami
Sanata mai wakiltar mazabar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, ya yi magana game da ba ‘yan Najeriya damar mallakar bindiga don kare kansu daga harin 'yan bindiga.
Wasu sojoji guda biyu sun samu nasarar kama wani mutum da ya ke amfani da kakin soja wajen damfarar mutane a Nasarawa. Sun kama shi ne a garin Awe da ke jihar.
Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar Ogun bayan tsallake katanga, kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar Talata. An fara nemansu.
'Yan fashi da makami sun dira kan wasu bankuna biyu a Ikere Ekiti, jihar Ekiti, kuma ana hasashen mutum uku ne suka rasa rayukansu a wanna farmakin.
An rawaito cewa Anas ya kashe abokinsa a watan Yunin shekarar 2017 bayan rikici ya barke tsakaninsa da Mukhtar kan Naira dari. Kotu ta ba da umurnin rataye shi.
Babbar kotu da ke zamata a Potiskum da ke jihar Yobe ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan daya daga cikin sojojin da ake zargi da kisan Sheikh Goni Aisami.
Yan bindiga sun kai farmaki kan motar kuɗin gidan gwamnatin jihar Ogun, sun yi awon gaba da makudan kudi tare da ajalin akantan ofishin Gwamna Abiodun.
Ana fama da barayi da ‘Yan bindiga a Najeriya, a haka ne wasu Sojoji sun dauke ‘dan jaridan fadar Shugaban kasa, sun yi masa fashi a Abuja a makon da ya wuce.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Sunusi Yusuf da wasu kan zargin hadin baki da yi wa abokinsu Nura Ibrahim fashin Naira miliyan 2.9.
Fashi da makami
Samu kari