Sanata Ya Gabatar da Kudirin Halatawa Mutane Mallakar Bindiga a Majalisa

Sanata Ya Gabatar da Kudirin Halatawa Mutane Mallakar Bindiga a Majalisa

  • Wani sanata daga Kudancin Najeriya ya gabatar da kudurin dokar ba 'yan Najeriya damar mallakar bindiga
  • Sanata Ned Nwoko mai wakiltar mazabar Delta ta Arewa ya ce mallakar bindiga zai ba mutane damar kare kansu
  • Sai dai wani mai fashin baki kan harkokin tsaro, Murtala Bashar da Legit Hausa ta zanta da shi, ya kalubalanci kudirin sanatan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Sanata mai wakiltar mazabar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, ya yi magana game da ba ‘yan Najeriya damar mallakar bindiga.

Sanatan a wata tattauna da Arise Tv a ranar Alhamis, ya kawo bukatar hakan la'akari da yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a kasar.

Kara karanta wannan

Babban nasara: Sojoji sun sheke 'yan ta'adda 185, sun kama wasu 212

Sanata Ned Nwoko mallakar makamai
Sanata Nwoko na neman majalisa ta ba 'yan Najeriya damar mallakar makami. Hoto: @Prince_NedNwoko
Asali: Facebook

Nwoko ya jaddada cewa kudirin da ya gabatar na kare kai da ka’idojin mallakar bindigogi zai magance wannan matsalar da ta addabi kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudurin dokar na jiran karatu na farko a majalisa

Ya zayyana ka’idojin cancantar mallakar bindiga da suka hada da, shaidar lafiyar kwakwalwa daga manyan likitoci guda biyu.

Ya ce: “Dole ne a gabatar da kudurin doka a majalisar dattawa da zai ba 'yan Najeriya damar mallakar bindiga.
"Kudiri na game da dokar kare kai da mallakar bindiga, yanzu haka na jiran karatu na farko, kuma ya yi magana kan matsalar tsaro da ta ta'azzara."

Matsalolin da ke tattare da ba mutane damar mallakar bindiga

Wani mai fashin baki akan harkokin tsaro, Murtala Bashar da Legit Hausa ta zanta da shi akan wannan lamari ya ce, akwai babbar illa tattare da wanna kudiri.

Kara karanta wannan

A kara hakuri: Minista ya ce ana daf da cin moriyar kudurorin Shugaba Tinubu a Najeriya

Murtala Bashar ya ce yawaitar bindigogi a hannun jama'a zai iya haifar da kashe-kashen farar hula yasu-yasu, musamman idan akwai bambancin addini ko ƙabilanci.

Ya ce ko kasashen da suka ci gaba irin Amurka, suna fuskantar wannan kalubalan, wanda ta sa kullum suke yaki akan ba mutane damar mallakar makaman.

A cewarsa:

"Idan ya zamana kowa zai iya mallakar bindiga, to kenan kowa zai iya kashe dan uwansa ya ce kare kansa ya yi. Wannan zai dawo da rigingimu na addini da kabilanci.
"Sannan a hannu daya akwai daukar rai, abin nufi, mutum zai dauki ransa da kansa idan ya shiga wata matsala, ko ayi kuskure yaro ya dauki bindigar ya harbi kansa ko wani a gidan."

Bashar ya ce ba mutane damar mallakar bindiga ba shi ne mafita ba, kamata yayi gwamnati ta bunkasa 'yan sanda wadanda su ne ke da alhakin tsaron farar hula.

Za a samar da makarantun koyon harbin bindiga

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya ta tsaida lokacin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima

Amma da yake jaddada bukatar samar da tsari mai kyau kan mallakar bindigar kamar yadda The Nation ta ruwaito, Sanata Ned Nwoko ya ce:

"Abin da nake kokarin yi a nan shi ne samar da tsarin da za a bai wa mutanen da ke son mallakar bindiga dama."

Kudirin dokar ya ba da shawarar samar da makarantun koyon harbin bindiga wadanda tsoffin jami’an soji za su tafiyar da su.

Nwoko ya ba da hujjar bukatar ba da damar mallakar bindigar bisa ga rashin tsaro da karancin matakan tsaro a yanzu.

Majalisa ta fara yi wa kundin mulkin 1999 kwaskwarima

A wani labari kuma, majalisar wakilan tarayya ta ce zuwa nan da shekarar 2025 za ta kammala gyara kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Majalisar ta ce za ta tabbatar ta sabunta kundin ta yadda zai shafi rayuwar al'ummar kasar tare da yin hakan akai-akai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel