Sojoji Sun Kama Sojan Boge a Nasarawa Da Ya Dade Yana Damfarar Mutane

Sojoji Sun Kama Sojan Boge a Nasarawa Da Ya Dade Yana Damfarar Mutane

  • Wasu sojoji guda biyu sun samu nasarar kama wani mutum da ya ke amfani da kakin soja wajen damfarar mutane a Nasarawa
  • An ruwaito cewa sojojin sun kama mutumin mai suna Haladu a garin Awe, kuma sun mika shi ga rundunar 'yan sandan jihar
  • Mutumin ya yi ikirarin cewa shi soja ne da ke aiki a Biu, jihar Borno, amma 'yan sanda sun gano sojan gona ne kuma dan damfara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Nasawa - Rundunar 'yan sanda a jihar Nasarawa sun ce sojojin Najeriya sun kama wani sojan gona a karamar hukumar Awe, inda suka mika shi ga rundunar don gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

A karshe, an cafke sojan da ya yi wa gwamnan APC rashin kunya, bayanai sun fito

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ya fitar da sanarwar hakan a ranar Alhamis a garin Lafia.

An kama sojan boge a Nasarawa
An kama sojan boge da ke damfarar mutane da sunan zai sama masu aikin soja a Nasarawa Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Dubun Haladu ta cika bayan haduwa da sojojin gaskiya

Nansel ya ce an kama sojan gonar ne bayan da dakarun sojin suka rinka bin diddigin sa na dan wani lokaci, jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Wasu sojoji biyu ne da suka je hutu gida suka kama wani Muhammed Haladu a bayan ginin otel din Ozas, yana sanye da kayan sojoji a karamar hukumar Awe.
"Da sojojin suka mika shi ga 'yan sandan Awe, sai ya ce shi jam'in soja ne karkashin bataliya ta 231 da ke Biu, jihar Borno, amma da aka tsananta bincike an gano sojan gona ne."

Yana damfarar mutane da sunan sama masu aikin soja

Sanarwar ta kara da cewa wanda aka kaman, an gano ya nemi aikin sojan bai samu ba, amma ya sayi kayan sojojin a wani barikin soji don gudanar da munanan ayyukansa.

Kara karanta wannan

Mutane 5 wadanda suka fi karfin fada-aji a gwamnatin Buhari da yanzu aka daina jin duriyarsu

A cewar sanarwar:

"Wanda aka kaman, yana damfarar mutane da sunan zai sama masu aikin soja, alhalin ya san ba shi da ikon daukar wani aikin."

Kwamishinan 'yan sanda ya jinjinawa jami'an soji

Daily Trust ta ruwauto jami'in hulda da rundunar 'yan sandan ya kuma ce jami'an sun kuma kama wani rikakken dan fashi da ya addabi jihar mai suna Kabiru Yusuf.

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar CP Umar Shehu Nadada ya jinjina wa kokarin jami'an sojin tare da kara masu kwarin guiwar yaki da ta'addanci a fadin kananan hukumomi 13 na jihar.

Mayakan ISWAP sun datse hannuwan wasu masunta a Borno

A wani labarin daga jihar Borno, mayakan ISWAP sun yanke hukuncin datse hannu kan wasu masunta guda biyu da suka ce sun sace masu kwandunan kifi guda biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa, masunta na daga cikin wata babbar kungiyar masu kamin kifi a Marte da ke jihar, kuma suna biyan mayakan ISWAP haraji don yin aikin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel