Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Kuɗin Gwamnati Sun Sace Makudan Kuɗi Tare da Kashe Hadimin Gwamna

Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Kuɗin Gwamnati Sun Sace Makudan Kuɗi Tare da Kashe Hadimin Gwamna

  • Yan bindiga sun kwace motar kuɗi ta gwamnatin jihar Ogun kuma sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe masu yawa ranar Laraba
  • Maharan waɗanda ake zargin ƴan fashi da makamai ne sun kuma kashe hadimin Gwamna Abiodun wande ke biye da kuɗin
  • Gwamnan na APC ya je ta'aziyya ga iyalan mamacin kuma ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin matarsa da yayansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Ogun - Wasu ƴan bindiga da ake zargin yan fashi da makamai ne sun farmaki motar dakon kuɗi mallakin gwamnatin jihar Ogun ranar Laraba.

Channels tv ta ruwaito cewa ƴan fashin sun yi awon gaba da maƙudan kuɗin da kawo yanzu ba a san adadinsu ba a harin.

Marigayi Oyekanmi da Gwamna Abiodun.
Yan bindiga sun kwace motar kuɗi, sun kashe hadimin gwamnan jihar Ogun Hoto: tvcnews
Asali: Twitter

Haka nan kuma maharan sun kashe Akantan ofishin Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, Taiwo Oyekanmi, wanda ya rako motar kuɗin a hanyar komawa ofis.

Kara karanta wannan

Gwamna Namadi ya koka, ya faɗi matsaloli 2 da suka fara takurawa mutane a jihar Jigawa

Kwamishinan rundunar yan sandan jihar, Abiodun Alamutu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce tuni ya bada umarnin toshe duk wata hanyar fita daga Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rundunar yan sanda ta tuntuɓi yan sanda makotan jihohi domin su taimaka wajen kama maharan da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Yadda lamarin ya faru

Bayanai sun nuna cewa Oyekanmi, daraktan kuɗi a ofishin gwamna ya ciro kuɗin da ba a bayyana yawansu ba daga wani reshen bankin Fidelity a Abeokuta, a hanyar komawa ofis maharan suka far masa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan, waɗanda suka kai mutum biyar, sun harbi hadimin gwamnan har lahira a daidai gadar ƙasa ta Kuto, kana suka sace kuɗin.

Wani jami'in gwamnati ya ce da farko an garzaya da Oyekanmi da sauran hadiman da suka samu rauni zuwa babban asibitin jiha da ke Ijaye, inda aka tabbatar akantan ya cika.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa manoma a gonakinsu, sun yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Taraba

A cewar majiyar, yan sandan da ke gadin akantan ba su tare da shi a lokacin saboda ya nemi izinin a bar shi ya warware wasu matsalolin iyali.

Gwamna Abiodun ya yi ta'aziyya

TVC News ta tattaro cewa Gwamna Dapo Abiodun ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayin kuma ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin matarsa da 'ya'yansa.

Ya kuma bayyana cewa waɗanda suka kashe mamacin ba zasu sha ba, zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da sun girbi abinda suka shuka.

Yan bindiga sun zagaye Jalingo

A wani rahoton Ƙungiyar mafarauta ta koka kan yadda 'yan bindiga sama da 300 suka kewaye Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Shugaban mafarauta na jihar, Adamu Ɗantala, ya ce kawo yanzu sun kashe jami'an tsaro mafarauta sama da 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel