Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Aisami a Yobe, Ta Ba da Dalilai

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Aisami a Yobe, Ta Ba da Dalilai

  • Babbar kotu da ke zamanta a Potiskum a jihar Yobe ta yi hukunci kan sojojin da ake zargi da kisan Sheikh Aisami
  • Ana zargin Gideon Adamu da John Gabriel da kisan malamin a shekarar 2022 a jihar Yobe bayan kokarin yi masa fashi
  • Mai Shari'a, Usman Zannah yayin sharia'r, ya yanke hukuncin kisa kan daya daga ciki John Gabriel ta hanyar rataya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Yobe - Babbar kotu a jihar Yobe ta yanke hukunci kan sojojin da ake zargi da kisan Sheikh Goni Aisami a jihar Yobe.

Kotun ta yanke hukuncin ne kan sojojinwadanda ake zargi, John Gabriel da Adamu Gideon kan zargin kisan kai da kuma fashi.

Kara karanta wannan

Maulidi: Atiku ya yi martani kan harin bam da aka yi kan bayin Allah a Kaduna, ya ba da shawara

Kotu ta yi hukunci kan sojojin da su ka hallaka Goni Aisami
Kotu ta Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wanda ake zargi da kisan Goni Aisami. Hoto: Sheikh Goni Aisami.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke kan sojan?

Wadanda ake zargin sun hallaka shehin malamin ne a watan Agusta na shekarar 2022 a jihar Yobe, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari'a, Usman Zannah yayin sharia'r, ya yanke hukuncin kisa kan daya daga ciki mai suna John Gabriel ta hanyar rataya

Yayin da Gideon Adamu kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan gyaran hali, cewar Leadership.

Ana zargin Gabriel da fashi da makami wanda hakan ya sabawa kundin laifuka da hukunci sashe na 221 na dokokin na jihar Yobe.

Wasu shaidu aka mika kotun yayin hukuncin?

Yayin da ake zargin Adamu da zargin kokarin kisan kai da kuma taimaka wa wurin aikata sata.

Yayin da ake hukuncin, masu kara sun gabatar da shaidu guda 12 wanda ke tabbatar da aikata laifin wadanda ake karar.

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu ba: Sojoji sun fusata Pantami da hadimin Buhari da kisan masu Maulidi

Har ila yau, wadanda ake karar sun tabbatar da aikata laifin inda su ka ki gabatar da wasu shaidu a karar.

Soja ya yi ajalin malamin addinin Musulunci

A wani labarin, wani shehin malami a jihar Yobe ya rasa ransa bayan ya taimaki wani soja bai sani ba.

Marigayin mai suna Sheikh Goni Aisami ya rasa ransa ne bayan sojan ya yi kokarin yi masa fashi da kuma hallaka shi.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Dungus Abdulkarim shi ya tabbatar da haka inda ya ce sun shiga hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel