Bidiyo: Yan Fashi Sun Farmaki Bankuna 2 a Ekiti, Sun Kashe Mutum 3 Tare da Sace Makudan Kudade

Bidiyo: Yan Fashi Sun Farmaki Bankuna 2 a Ekiti, Sun Kashe Mutum 3 Tare da Sace Makudan Kudade

  • 'Yan fashi da makami sun dira kan wasu bankuna biyu a Ikere Ekiti, jihar Ekiti, sun kai harin ne a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba
  • Da misalin karfe 5 na yamma aka ruwaito 'yan fashin sun shiga bankunan, inda ake hasashen mutane uku ne suka rasa rayukansu
  • Jaridar Legit ta ci karo da bidiyon yadda 'yan bindigar suka gudanar da aikin a shafin X (tsohuwar Twitter), harin da suka yi a idon mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ikere, Ekiti state - Akalla mutum uku ake tunanin sun mutu yayin da 'yan fashi suka dira kan wasu bankuna biyu a garin Ikere-Ekiti, shelkwatar karamar hukumar Ikere, jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Manyan hare-hare 8 da sojoji suka kai wa farar hula ta sama a cikin shekaru 6 a Najeriya

Rahoton The Nation, ya nuna cewa kungiyar 'yan fashi ta 'daredevil' da suka kai 20 sun dira garin misalin karfe 5 na yamma, inda suka yi fashi a bankuna biyu.

Yan fashi sun dira kan bankuna biyu a Ekiti
'Yan fashin sun ci karen su ba babbaka yayin da suka kai hari a bankunan jihar Ekiti, sun kashe mutum uku. Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

Ekiti: Mutane sun mutu a fashin bankunan Ikere

Jaridar Nigerian Tribune ta ce Oba Adejimi Alagbado, sarkin Ikere Ekiti, ya nuna kaduwarsa kan wannan fashin, inda ya kira hakan babban ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya ce abin takaicin shi ne 'yan fashin sun ci karen su ba babbaka na tsawon mintuna ba tare da jami'an tsaro sun kawo dauki ba, duk da akwai sojoji da 'yan sanda a kusa.

Sarki Alagbado ya ce:

"Na kira D.P.O na rundunar 'yan sanda, ya tabbatar mun da cewa sojojin da ke yankin suna da masaniya, amma har 'yan fashin suka gama ta'adin su babu jami'in tsaron da muka gani."

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Mahara sun sace babban Sarki bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin hana garkuwar

Sai dai duk wani yunkuri na tuntubar Sunday Abutu, jami'in rundunar 'yan sanda na jihar Ekiti kan lamarin ya ci tura.

Kalli bidiyon harin a kasa:

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a dajin Kaduna

A wani labarin, dakarun sojin kasa sun yi nasarar fatattakar wasu 'yan ta'adda daga dajin Kaduna, inda suka kwato babura da makamai, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Wannan na daga yunkurin sojojin na kakkabe duk wasu 'yan ta'adda da ke buya a dazukan Kaduna, tare da tabbatar da wanzuwar tsaro a jihohin Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel