Tashin Hankali Yayin da Fursunoni 3 Suka Tsere Daga Gidan Gyaran Hali Na Ogun, an Fara Farautarsu

Tashin Hankali Yayin da Fursunoni 3 Suka Tsere Daga Gidan Gyaran Hali Na Ogun, an Fara Farautarsu

  • Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar Ogun bayan tsallake katanga, kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar Talata
  • Sai dai hukumar gidajen gyaran hali ta kasa reshen jihar Ogun ta ce tserewar fursunonin ba fashin magarkama ba ne
  • Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka tseren an yanke masu hukunci kan laifukan da suka shafi fashi da makami, kisan kai da fyade

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ogun - Wani sabon labari na nuni da cewa wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyara hali na Ijebu Ode da ke karamar hukumar Ijebu Ode, jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa fursunonin sun tsallake katanga tare da arcewa a safiyar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Inna lillahi: An sake kai hari wata jihar Arewa, an kashe mutum biyu tare da yin mummunar barna

Fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali na Ogun
Fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali a Ogun, an fara farautarsu. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Fursunonin su ne:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hammed Adeboyejo wanda aka yanke wa hukunci kan fashi da makami da kuma kisan kai, Fatai Taiwo Akande shi ma laifin kisan kai, da kuma Aliu Oguntona wanda aka daure shi akan laifin fyade.

Fashin magarkama ne ya kai ga tserewar fursunonin?

A ciki wata sanarwa daga kungiyar tsaro ta So-Safe reshen Ijebu Imushin, an tabbatar da tserewar fursunonin tare da neman jama'a su ba da rahoto da zaran sun gan su, rahoton The Guardian.

Mai magana da yawun hukumar gidajen gyaran hali na Najeriya, reshen jihar Ogun, Victor Oyeleke ya tabbatar da lamarin ya yi zantawa da Daily Trust a ranar Talata.

Oyeleke ya ce:

"Tuni aka tura jami'ai don nemo fursunonin biyu tare da mayar da su gidan gyara halin. Muna da shacin yatsan su tare da lambobin iyalansu, kuma muna aiki tare da sauran jami'an tsaro."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari ana shirin taron addini a arewa, sun kashe sama da 15

Ko da aka tambaye shi ko tserewar fursuninin ya faru sakamakon fashin magarkama, ya ce "Ba haka bane, fashin magarkama shi ne idan suka farmaki gidan yarin"

Ya ba da tabbacin cewa za a cafke wadanda suka tseren nan ba da wani dogon lokaci ba.

Babatunde Lemo zai fadi yadda Emefiele ya mallaki bankin Union

A wani labarin, bincike kan yadda Godwin Emefiele ya mallaki bankin Union ya dauki sabon salo yayin da aka gayyaci shugaban bankin Titan Trust.

Babban mai bincike kan badakalar da aka tafka a CBN na zargin an yi amfani da Babatunde Lemo da wasu wajen mallakar bankin Union.

Asali: Legit.ng

Online view pixel