Na Taba Satar Adaidaita Sahu Sau Daya, In Ji Shahararren Mawakin a Najeriya, Ya Bayyana Dalili

Na Taba Satar Adaidaita Sahu Sau Daya, In Ji Shahararren Mawakin a Najeriya, Ya Bayyana Dalili

  • Shahararren mawaki a Najeriya, Akinbiyi Abiola Ahmed ya fadi abubuwan da ya aikata a baya marasa kyau da ya yi dana sani
  • Mawakin wanda aka fi sani da Bella Shmurda ya ce har satar adaidaita sahu ya yi don samun kudaden da zai bunkasa harkokin wakarsa
  • Fitaccen mawakin ya ce neman suna ta ko wane hali ya saka shi yarjejeniya da wani kamfani wanda abin bai kare da dadi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Fitaccen mawaki a Najeriya, Akinbiyi Abiola Ahmed da aka fi sani da Bella Shmurda ya bayyana abubuwa marasa kyau da ya yi a baya.

Bella ya ce a lokacin da ya ke kokarin tashe, ya taba satar adaidaita sahu don bunkasa harkar wakarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Mawaki ya bayyana yadda ya yi kwacen adaidaita sahu lokacin da ya ke tashe
Bella Shmurda ya daba sanin abubuwa marasa kyau da ya aikata a baya. Hoto: Abiola Ahmed.
Asali: Instagram

Wasu abubuwa marasa kyau Bella ya aikata a baya?

Har ila yau, ya ce neman suna ta ko wane hali ya saka shi yarjejeniya da wani kamfani wanda abin bai kare da dadi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya ce kasancewarsa uba ya saka shi zabar irin wakokin da zai yi da kuma faifan bidiyo da ya kamata ya fito, cewar WeTalkSound.

A cewarsa:

"Bai kamata na yi gaggawa ba, kowa ya na sauri, na yi abubuwa wanda daga baya ba su ba da abin da ake bukata ba."

Ya yi magana kan kasancewsa mahaifi a harkar wakoki

Ya kara da cewa:

"Na taba satar adaidaita sahu, amma yanzu alhamdulillah da halin da na ke na ci gaba.
"Ganin yaro na ya na karamin karfin gwiwa, menene yaron zai iya gani a nan da shekaru 10, ba na son ya kalli wasu bidiyon wakoki na da ba su dace ba, inason ya ga sabon Bella."

Kara karanta wannan

Matashi ya bugo keke daga jihar Benue don ziyartan Ahmed Musa a gidansa

Bella ya shahara ne a shekarar 2019 bayan sake wata waka mai suna 'Vision 2020' da sauran wakoki da ya fitar daga baya.

Kotu ta umarci kama Gwanja a Kano

Kun ji cewa fitaccen mawakin Kannywood, Ado Isa Gwanja ya sake shiga matsala bayan umartar kama shi da kotu ta yi.

Ana zargin Gwanja da yin wasu wakoki wadanda ba su dace ba da ake ganin sun saba al'adun Bahaushe da kuma rusa tarbiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel