Yadda Aka Yi Garkuwa da Ni Bayan Fitowa Daga Aiki Inji ‘Dan Jaridan Fadar Shugaban Kasa

Yadda Aka Yi Garkuwa da Ni Bayan Fitowa Daga Aiki Inji ‘Dan Jaridan Fadar Shugaban Kasa

  • Wani ‘dan jarida da yake aiki a fadar shugaban kasa ya bada labarin arangamarsa da wasu miyagun mutane a Abuja
  • Bayan ya tashi daga aiki a Aso Rock wata rasa, tsautsayi ya jawo masa fada hannun wadanda su ka yi masa fashi
  • A sanadiyyar haka ya rasa kudin da ke cikin bakinsa, komfuta, takardun aiki da kuma kudin wani da yake hannunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Daya daga cikin ‘yan jaridan da hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta tura Aso Rock Villa ya shiga hannun ‘yan bindiga.

‘Dan jaridan ya bada labarin yadda ‘yan bindiga su ka dauke shi a Abuja, Daily Trust ta kawo labarin yadda abin ya auku a cikin makon nan.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi barna a Kaduna, sun sungume Hakimi a sababbin hare-hare

‘Dan jaridan ya yi kuskure ne wajen shiga mota, ya burma motar 'yan fashi bayan ya tashi daga wurin aiki, zai koma gidansa a wajen Abuja.

Abuja
An addabi mutanen Abuja da sata Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu wannan Bawan Allah bai dawo daidai, cike yake da firgicin abin da ya faru.

Abin da ya faru da 'dan jaridan Aso Rock

"A ranar da ake magana, na yi aiki a fadar shugaban kasa. Bayan gama aiki na, na aika labarina sai na yanke shawarar tafiya gida.
Wani cikin Darektocin Aso Villa ya zabi ya ragewa ni da mai daukar hoto hanya zuwa sakatariyar gwamnati inda za mu shiga motocin hanya.
Ina zama ne a karkara, sai na je yankin ma’aikatar kudi kafin in dauki mota zuwa gadar Dantata daga nan kuma sai in tafi gidana.
Da karfe 4:45 na yamma ne. Nayi kokari kar in shiga motar da bai daidai ba saboda yawan labaran masu garkuwa da mutane a Abuja."

Kara karanta wannan

Yadda matashi dan shekaru 20 ya kashe mahaifinsa a Kaduna

- 'Dan jaridan

A haka ‘dan jaridar ya shiga motar wani da ya yi masa kama da jami'in gwamnati, cikin fasinjojin akwai mai kama da ma’aikacin banki.

'Dan jarida a hannun miyagu

Matsalar ta fito fili da wata mata ta hau motar domin a kai ta Lugbe, tun nan ‘dan jaridar ya nuna ya yi mantuwa zai sauka, hakan bai yiwu ba.

A cewarsa ‘yan cikin motar sun latse shi, su ka rika gudu saboda a hana shi fita, a nan ne su ka yi masa barazanar cewa za su hallaka shi.

"Su ka matse ni, su ka tambayi inda na ke zama. Jikina ya na rawa, su ka lalube jaka ta, su ka dauke N375, 000, agogo da katin bankin GTB.
Sun kuma dauke komfuta ta, $200, na’urar caji, takardar shiga Aso Rock, katin zama ‘dan kungiyar NAN, kudi da wasu dukiyoyi masu daraja."

- 'Dan jarida

N13m za ta ceci 'dan jarida

Kara karanta wannan

Dan caca da ya ciyo N102m zai taimakawa dalibin da yayi asarar kudin karatunsa a caca

‘Dan jaridan ya ce miyagun wadanda su ka shaida masu su sojoji ne sun bukaci ya biya N13m a matsayin kudin fansa domin ya ceci kan shi.

Da aka matsa domin ya kawo kudi sai ya nuna bai da shi, aka dauki katin bankinsa aka cire kudi, amma su ka nuna ba za su hallaka shi ba.

Zuwa lokacin da su ka sake shi, an dauke N505,000 daga cikin asusun bankin na shi. Ba wannan ne karon farko da aka ji an yi fashi a Abuja ba.

Sata a birnin Abuja

Kwanaki aka samu labari an sace wayar ‘Dan takaran jam’iyyar APGA a zaben gwamnan jihar Nasarawa a kotun daukaka kara da ke Abuja.

A yammacin Laraba Kotun ta zauna domin sauraron shari’ar zaben Gwamna Abdullahi Sule da ‘dan takaran PDP watau David Ombugadu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel