Yan Sanda Sun Yi Artabu da 'Yan Fashi a Jihar Ogun, An Jikkata Mutum 2

Yan Sanda Sun Yi Artabu da 'Yan Fashi a Jihar Ogun, An Jikkata Mutum 2

  • 'Yan sanda sun fatattaki wasu yan fashi da suka kai hari Otal ranar Jumu'a a ƙaramar hukumar Sagamu ta jihar Ogun
  • Kakakin yan sandan jihar ta ce dakaru sun samu labarin yan fashi sun shiga wani Otal, suka kai ɗauki kuma aka yi musayar wuta
  • Ɗan sanda mai muƙamin Insufekta da masu gadi biyu sun jikkata yayin fafatawa kuma an garzaya da su Asibiti

Jihar Ogun - Wasu mahara da ake kyautata zaton 'yan fashi da makami ne sun yi musayar wuta da dakarun rundunar 'yan sanda a jihar Ogun ranar Jumu'a.

'Yan fashin sun gwabza da 'yan sandan ne yayin da suka yi yunƙurin yin fashi a wani Otal a garin Sagamu, ƙaramar hukumar Sagamu ta jihar Ogun.

Jami'an yan sandan Najeriya.
Yan Sanda Sun Yi Artabu da 'Yan Fashi a Jihar Ogun, An Jikkata Mutum 2 Hoto: PoliceNG
Asali: UGC

An tattaro cewa ‘yan fashi da makamin sun harbi insufektan ‘yan sanda guda daya da masu gadi biyu yayin musayar wuta da jami'an 'yan sandan da suka kai ɗauki.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Ɗauki Mataki Mai Jan Hankali Kan Sace Ɗalibai Mata a Jami'ar Arewacin Najeriya

Rahoton Daily Trust ya gano cewa an ɗauki ɗan sanda da masu gadin da suka ji raunuka zuwa Asibitin koyarwa na jami'ar Olabisi Onabanjo Teaching Hospital (OOUTH) a Sagamu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar 'yan sanda ta yi magana kan lamarin

Jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar 'yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da aukuwar lamarin ga 'yan jarida a Abeokuta.

Ta ce dakarun ‘yan sandan ofishin Sagamu sun samu kiran gaggawa ta waya da misalin karfe 1:00 na tsakar dare cewa ‘yan fashi sun shiga Otal din Remo Majestic da ke Sagamu.

Kakakin 'yan sandan ta ƙara da cewa bayan samun rahoton, nan take aka haɗa tawagar dakaru suka durfafi wurin domin kai ɗauki.

Vanguard ta rahoto Odutola na cewa:

"Suna ganin zuwan dakarun 'yan sanda, 'yan fashin ba su yi wata-wata ba suka buɗe musu wuta yayin da jami'an suka maida martani aka fara artabu."

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Mata da Miji da 'Ya'yansu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki Mai Ƙarfi a Jihar Arewa

"Biyu daga cikin maharan sun ji munanan raunuka yayin da sauran suka arce zuwa cikin daji mafi kusa ɗauke da raunukan alburusai."

Ta kara da cewa "wadanda ake zargin 'yan fashi da makami ne sun shiga cikin mutane sun yi cudanya da masu kwana kafin su kai harin."

Yan Sanda Sun Yi Karin Bayani Kan Mutuwar Mawakin Najeriya

A wani rahoton kuma Har yanzu rundunar yan sandan Najeriya na ci gaba da gudanar da bincike a kan mutuwar makwai Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Idowu Owohunwa, ya yi jawabi a ranar Juma'a inda ya yi karin haske kan inda suka kwana a bincike kan mutuwar mawakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel