‘Yan Fashi Sun Yi Shigan ‘Yan Sanda, Sun Yi Fashin Miliyoyin Kudi Ido Ya Na Ganin Ido

‘Yan Fashi Sun Yi Shigan ‘Yan Sanda, Sun Yi Fashin Miliyoyin Kudi Ido Ya Na Ganin Ido

  • An samu wasu miyagun ‘yan fashi da su ka raba wani ‘dan shekara 60 da kudinsa bayan ya fito daga cikin banki
  • ‘Yan fashin sun sa wa mutumin ido ne har su ka rutsa shi a kan hanya, jama’a su na kallo wannan abin ya faru a Ilorin
  • Abin da ya bada mamaki shi ne wadanda su ka yi fashi da makamin da maraice su na cikin kayan dakarun ‘yan sanda

Kwara - Wasu ‘yan fashi da makami sun aukawa wani bawan Allah a jihar Kwara, su ka yi nasarar yi masa awan gaba da makudan kudi.

A labarin da Daily Trust ta fitar, an fahimci wannan lamari ya auku ne a layin Lajorin da ke kusa da babban kotun jiha da ke garin Ilorin.

Miyagun ‘yan fashin su uku sun zo ne dauke da bindigogi na AK-47, su ka tare wannan mutum mai shekara 60 sa'ilin rana ta na fadawa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Kafa Doka Kan 'Yan Bola Jari Da Masu Baban Bola Shiga Yankunan Abuja, Ya Fadi Matakin Gaba

‘Yan Fashi
Hoton wasu ‘yan fashi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Yan fashi sun yi ta'adi a 'yan mintuna

Abin da ya fi ba mutane mamaki shi ne da kimanin karfe 6:50 na yamma aka yi wannan danyen aiki, kafin ayi wani yunkuri, sun tsere.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani wanda abin ya faru gaban idanunsa, ya shaidawa jaridar cewa abin ya faru kamar wasan kwaikwayo, bai bari an kama sunansa ba.

Mutane sun ce ‘yan fashin su uku sun zo a wata mota kirar Toyota Corolla ta shekarar 2016 mai launin toka dauke da lambar jihar Legas.

"Su na dauke da kayan ‘yan sanda har na dauka jami’an tsaro ne, da farko na dauka wanda aka yi wa fashin ‘dan Yahoo ne.
Har ina fada masu su yi masa a hankali, sai daga baya na fahimci ashe tantiran miyagu ne, sai na lallaba na tsere daga wurin.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin Jihohi 3 Da Suka Dauki Fiye Da Wa'adin Shekaru 8 a Ofis a Tarihi

Shi ma wanda aka yi wa fashi da makamin ya na cikin mota wata shudiyar Toyota Corolla 2006.

- Wanda ya bada shaida

'Yan fashi sun biyo shi daga banki

Vanguard ta ce ‘yan fashin sun yi ta bibiyar shi ne daga wani banki, da su ka rutsa shi a kan titi, sai su ka bukaci ya kawo kudin da ya karbo.

Masu shaguna sun tashi da wuri a ranar saboda gudun ‘yan sanda su kawo masu farmaki. ‘Yan sanda ba su ce komai ba tukuna har yanzu.

Kamfanin BUA an yi ba ayi ba

A daidai lokacin da aka ji labari cewa ragin farashin siminti da kamfanin BUA ya yi almara ce kawai, sai ga shi kayan abincinsu sun kara tsada.

Ba tare da bada wata sanarwa ba, ana zargin BUA ya tashi farashin fulawa, sukari da taliyarsa jim kadan bayan karya buhun siminti zuwa N3500.

Asali: Legit.ng

Online view pixel