Abuja
Gowon ya ce Yarjejeniyar Aburi ta rushe saboda Ojukwu na son ikon soji a yankuna. Ya ce rashin halartar taron Benin da Ojukwu ya yi ya ƙara rura wutar yaƙin basasa.
Gwamnatin tarayya za ta kwashe 'yan Najeriya daga Isra'ila da Iran saboda tsanantar rikici. Ofisoshin jakadancin Najeriya na aiki don tabbatar da tsaron kowa.
APC na shirin mamaye kananan hukumomin FCT a zaɓen ciyamomi na 2026 da 2027, tare da tsananta dabarun jawo 'yan adawa. INEC za ta gudanar da zaɓen FCT a Fabrairu.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikƙo Umaru Radda ya samu lambara yabo ta gwamna mafi aiki a shekarar 2025, an yaba masa bisa yadda yake kawo ci gaba.
tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Bola Tinubu yana ikirarin dimokuradiyya yana yana take ta. Ya ce Tinubu na shirin dagula tarihin 12 ga Yuni.
Ministan sadarwa a mulkin Buhari, Adebayo Shittu ya yi gargadi kan batun ajiye Kashim Shettima a 2027. Ya ce APC za ta shiga rudani idan aka ajiye Shettima.
PENGASSAN ta zargi dillalan fetur da tsadar mai, duk da faduwar farashin danyen mai a duniya. Kungiyar ta ce ya kamata fetur ya koma N700 zuwa N750.
Farfesa Wole Soyinka ya bukaci Bola Tinubu ya kaddamar da bincike kan kisan Kudirat Abiola, Bola Ige da Dele Giwa duk da karrama su da ya yi da lambar yabo.
Hukumar gudanarwa ta Abuja watau FCTA ta shirya kaddamar da fara aikin gina hediwaktar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, lauyoyi sun fara martani.
Abuja
Samu kari