Sanata Natasha Ta Gurfana a Kotu, Alkali Ta Yi Hukunci kan Bukatar Tsare Ta a Kurkuku

Sanata Natasha Ta Gurfana a Kotu, Alkali Ta Yi Hukunci kan Bukatar Tsare Ta a Kurkuku

  • Kotu ta bayar da belin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan N50m, bayan kin karbar buƙatar gwamnati na tsare ta a gidan yari
  • Gwamnatin tarayya na tuhumar Sanata Natasha da yin ƙarya cewa Sanata Godswill Akpabio da Yahaya Bello na kitsa kashe ta
  • Shugaban majalisar dattawa da tsohon gwamnan jihar Kogi suna daga cikin shaidun da gwamnati za ta gabatar a yayin shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da belin sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, a kan Naira miliyan 50.

A hukuncin da Mai Shari’a Chizoba Orji ta yanke hukunci kan buƙatar gwamnatin tarayya na garkame wacce ake kara a gidan yari.

Kotu ta amince da bukatar ba da belin Sanata Natasha, ta ki tsare 'yar majalisar a gidan yari
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gurfana gaban kotun tarayya, Abuja. Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Kotu ta ba da belin Sanata Natasha Akpoti

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnati ta nemi kotun ta tsare Sanata Natasha, wadda ake ƙara bisa tuhume-tuhume uku, a gidan yari har sai an kammala shari’ar ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari’a Orji ta bayyana cewa ba ta ga wani dalili na hana wadda ake ƙara belinta ba, tana mai cewa akwai isassun shaidu da ke nuna cewa ba za ta tserewa shari’ar ba.

Sakamakon haka, ban da kudin beli na N50m, kotun ta umurci Sanata Natasha ta kawo mutum ɗaya da zai tsaya mata, kuma dole ne ya zama mai mutunci kuma mai kadarori a Abuja.

Kotun ta yanke hukuncin ne bisa dogara da sashi na 36 na kundin tsarin mulkin 1999, da kuma sashi na 163 da 165 na dokar gudanar da Shari’ar Laifuka ta 2015.

Daga baya, Mai Shari’a Chizoba Orji ta ɗage shari’ar har zuwa ranar 23 ga watan Satumba don fara shari'ar, inji rahoton Punch.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Natasha

Gwamnati na tuhumar Natasha ne kan zargin cewa ta yi ƙaryar cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, suna kitsa hirin kashe ta.

A cikin tuhumar mai lamba: CR/297/25, gwamnatin tarayya ta yi zargin cewa Sanata Akpoti-Uduaghan, wacce aka lissafa a matsayin ita kaɗai ce wadda ake ƙara, ta yi kalaman ƙarya da ɓatanci lokacin da ta ke bayani a wai gidan talabijin.

A cewar tuhumar, ta hanyar yin irin wannan zargi na ƙarya wanda ya ɓata sunan wasu, Sanata Akpoti-Uduaghan, ta aikata laifi a ƙarƙashin sashi na 391 na Dokar Laifuka, Cap 89, Dokokin Tarayya, 1990.

Haka kuma, bayanin tuhumar ya ƙara da cewa laifin da ake zargin 'yar majalisar da shi yana da hukunci a ƙarƙashin sashi na 392 na wannan dokar.

Sanata Godswill Akpabio da Yahaya Bello za su ba da shaida kan zargin da ake yi wa Sanata Natasha
'Yar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Akpabio, Yahaya Bello za su ba da shaida

Da take bayar da cikakken bayani game da laifin, gwamnatin tarayya ta shaida wa kotun cewa wadda ake ƙara ta aikata laifin da ake zargi a ranar 3 ga Afrilu, a lokacin watsa shirye-shiryen kai tsaye na Channels TV.

Daga cikin waɗanda aka lissafa a matsayin shaidu a cikin lamarin, sun haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta ce za ta gabatar da tsohon gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello, domin ba da shaida, duk da cewa suna daga cikin masu ƙara.

Sauran wadanda aka shirya don ba da shaida a shari'ar sune jami'an 'yan sanda biyu da suka binciki lamarin, Maya Iliya da Abdulhafiz Garba; Sanata Asuquo Ekpenyong da kuma Sandra Duru.

'Yan bindiga sun farmaki gidansu Natasha

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ƴan bindiga sun sake kai hari gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a jihar Kogi, amma an kama ɗaya da ake zargi da hannu a lamarin.

Rahoton da aka samu ya bayyana cewa wanda ake zargi, Joe Suberu, ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa wannan shine karo na uku da ya kai hari gidan.

Ofishin Sanata Natasha ya tabbatar da cewa matasan unguwar tare da haɗin gwiwar jami'an ƴan sanda, sun kawo ɗauki cikin gaggawa, inda suka yi nasarar fatattakar maharan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.