Shettima: Yadda Tinubu Ya Yi Aiki da Mataimaka 3 da Ya ke Gwamnan Legas

Shettima: Yadda Tinubu Ya Yi Aiki da Mataimaka 3 da Ya ke Gwamnan Legas

  • Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa kasancewar Bola Ahmed Tinubu ya yi aiki tare da mataimaka uku a jihar Legas ba ya nuna cewa zai sauya mataimaki
  • Bayo Onanuga ya karyata rade-radin cewa Tinubu yana shirin cire Kashim Shettima, yana mai cewa babu wata matsala tsakanin shugaban da mataimakinsa
  • Ya kuma ce tikitin Muslim Muslim ba matsala ba ce yanzu, domin tsoron da mutane ke da shi a baya na cewa za a mamaye wasu addinai ya riga ya gushe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai bayyana wanda zai kasance mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba sai bayan taron APC na 2026.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce game da yiwuwar cire mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, daga tikitin takara na APC a zabe mai zuwa.

Bola Tinubu yayin da ya ziyarci jihar Kaduna
Bola Tinubu yayin da ya ziyarci jihar Kaduna ranar Alhamis. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A wata hira da jaridar Daily Trust, Bayo Onanuga ya fadi dalilin da ya sanya Bola Tinubu sauya mataimaka da ya ke gwamna a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa Tinubu ya sauya mataimaka a Legas?

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya yi watsi da ikirarin cewa Tinubu yana da halin canza mataimaka.

Onanuga ya yi magana yana mai cewa abubuwan da suka faru a lokacin da yake gwamnan Legas sun samo asali ne daga matsalolin siyasa da rashin jituwa.

“E, lokacin gwamnan Legas ne, akwai matsala tsakaninsa da Kofoworola Bucknor-Akerele, wanda hakan ya kai ga barinta.
"Daga bisani Femi Pedro ya maye gurbinta, amma shi ma ya fice daga jam’iyya yana neman ya zama gwamna."

Rahoton Tribune ya nuna cewa bayan tsige Femi Pedro, majalisar Legas ta nada Abiodun Ogunleye domin ya maye gurbinsa a 2007.

Rahotanni sun nuna cewa Ogunleye ya shafe kwanaki 17 ne kawai a mataimakin Tinubu kafin wa'adinsu ya kare.

Onanuga: “Babu sabani tsakanin Tinubu da Shettima”

Onanuga ya ce akwai kyakkyawar fahimta tsakanin shugaban ƙasa da mataimakinsa, Kashim Shettima, kuma duk wata jita-jita da ake yadawa ta rashin jituwa ba ta da tushe.

Bayo Onanuga ya ce wasu mutane ne kawai suke yada jita jitar domin rudar mutane ba tare da wata hujja

Makomar tikitin Muslim Muslim a 2027

Onanuga ya ce batun tikitin Musulmi da Musulmi wanda Tinubu da Shettima suka tsaya da shi a 2023 ba shi da matsala, domin damuwar da mutane ke da ita a baya ta riga ta gushe.

Onanuga ya ce:

“Shugaban ƙasa ma ya halarci bikin nadin Fafaroma a Rome, Kiristoci suna rayuwarsu lafiya.
"Kuma yawancin mutanen da ake hasashen za su zamo mataimakansa duk Musulmi ne. Don haka, wannan batu ya wuce,”
Fadar shugaban kasa ta ce babu maganar sauya Shettima a 2027
Fadar shugaban kasa ta ce babu maganar sauya Shettima a 2027. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

SDP ta ce za ta kayar da Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar SDP ta ce tana shirye shiryen korar Bola Tinubu da APC a zaben 2027.

Shugaban APC na jihar Ebonyi ya ce kamar yadda aka kayar da PDP da Goodluck Jonathan a 2015, haka za a kayar da APC.

Legit ta rahoto cewa shugaban ya ce 'yan Najeriya za su sha mamaki game da manyan 'yan siyasar da za su tsaya takara a SDP a zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng