Dikko Radda Ya Lashe Lambar Yabo, Ya Zama Gwamna Mafi Aiki a 2025

Dikko Radda Ya Lashe Lambar Yabo, Ya Zama Gwamna Mafi Aiki a 2025

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya lashe lambar yabo ta gwamnan da ya fi kowane aiki a shekarar 2025
  • Aso Multimedia ce ta ba gwamnan wannan lambar yabo domin yabawa kokarin da yake wajen kawo ci gaba da fannoni daban-daban a Katsina
  • Kwamishinar harkokin mata ta Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta faɗi wasu daga cikin ayyukan da Dikko Raɗɗa ya yi a shekaru biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya lashe lambar yabo ta “gwamna mafi aiki na shekarar 2025” daga Aso Multimedia.

An ba da wannan gagarumar lambar yabo ne a wani biki mai kayatarwa da aka shirya a Abuja a ranar 13 ga Yuni, 2025.

Gwamna Dikko Radda ya samu lambar yabo.
Gwamna Dikko Radda ya lashe kyautar gwarzon shekara na 2025 Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Sakataren watsa labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulaha Mohammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an karrama Gwamna Radda ne bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen sauya Jihar Katsina ta fuskar inganta ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, tsaro da ƙarfafa tattalin arziki.

An ba Gwamna Dikko lambar yabo a Abuja

Kwamishinar harkokin mata, Hajiya Hadiza Yar’adua, tare da daraktan tsare-tsaren gwamna, Alhaji Umar Bishir Ibrahim, ne suka wakilci Dikko Raɗda wurin taron.

Gwamnan ya sadaukar da wannan kyauta ga jajirtattun mata, matasa masu buri, ma’aikata masu himma da kuma daukacin al’ummar Jihar Katsina.

Da take karɓar kyautar a madadin gwamna, Hajiya Hadiza ta ce lambar yabon ta ƙara nuna salon mulki da Gwamna Radda ke tafiya da shi, wanda ya ginu kan tausayawa, gaskiya da sadaukar da kai.

Wasu daga cikin ayyukan Gwamnan Katsina

Daga cikin manyan nasarorin gwamnatin Malam Dikko Radda da kwamishinar matan ta zayyano akwai:

  • Wakilcin mata: Tsarin ware kashi 30% na wakilcin ga mata a gwamnati.
  • Tallafin mata: Ware biliyoyin Naira na tallafi ga mata, shirin kiwon akuya, abinci da lafiyar uwa da jariri.
  • Lafiya: Gyaran cibiyoyin lafiya a matakin farko da gina asibitin kwararru mai na’urorin bincike na zamani.
  • Noma: Kaddamar da tsarin noman rani, raba dubban tan na takin zamani da kafa Cibiyar haɓaƙa noman zamani.
  • Ilimi: Daukar malaman makaranta sama da 7,000 ta shirin S-Power, da kuma biyan kuɗin jarrabawar WAEC, NECO da NABTEB ga ɗalibai fiye da 54,000.
  • Tsaro: Kafa rundunar Katsina Community Watch Corps da ta ɗauki jami’ai 1,500, tare da kaddamar da sabbbin motocin sintiri da kayan aiki don yakar ‘yan bindiga.
  • Titi da sufuri: Ginin sababbin hanyoyi da inganta sufuri a faɗin jihar Katsina.

An ba Dikko Radda lambar yabo.
An bayyana wasu daga cikin ayyukan da Dikko Radda ya yi a Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Hajiya Hadiza ta ƙara da cewa:

“Wannan lambar yabo ta ƙara nuna cewa shugabanci nagari yana yiwuwa idan shugabanni sun saurara, sun tsara kuma sun yi aiki da zuciya ɗaya don jin daɗin al’umma."

Dikko Raɗɗa ya yi magana kan nauyin shugabanci

A wani labarin, kun ji cewa Malam Dikko Raɗɗa ya ce shugabanci amana ce ba kofin gasa ba, yana mai cewa zai ci gaba da kokarin sauke nauyin al'umma.

Gwamna Radda ya ja hankalin shugabanni da cewa ya zama dole su jure suka da kalaman cin mutunci daga wasu ‘yan ƙasa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Katsina ranar Alhamis, a wani taron addu’a na musamman da gwamnatinsa ta shirya domin cika shekaru biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262