Babban Jigo a Kano, Buharin Dala Ya Gamu da Tsautsayi, Ya Rasu a Hanyar zuwa Wurin Atiku
- Wani jigon siyasa a Kano, Injiniya Mahmoud Sani Madakin Gini, wanda aka fi sani da Buharin Dala ya riga mu gidan gaskiya a hatsarin mota
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi jimamin rasuwar Buharin Dala, wanda ya ce yana hanyar zuwa kai masa ziyara a Abuja
- Atiku, jagoran ƴan adawa a Najeriya ya mika sakon ta'aziyya tare da addu'ar Allah ya jikan Buharin Dala, ya ba iyalai, ƴan'uwa da masoyansa haƙuri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala kuma jigon siyasa a jihar Kano, Injiniya Mahmoud Sani Madakin Gini ya rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar zuwa Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana jimami game da rasuwar Engr Mahmoud Sani Madakin Gini, wanda aka fi sani da Buharin Dala.

Asali: Twitter
Alhaji Atiku ya tabbatar da rasuwar Buharin Dala a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Tuwita, ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da Atiku ya shiga kan rasuwar Buharin Dala
Jagoran ƴan adawar Najeriya ya ce labarin ya girgiza shi matuƙa, musamman duba da cewa marigayin ya shirya kai masa ziyarar ban girma kafin faruwar hatsarin.
Alhaji Atiku ya ce:
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Na samu labarin rasuwar Engr Mahmoud Sani Madakin Gini (Buharin Dala) cikin baƙin ciki. Ya rasu ne a hatsarin mota yayin da yake kan hanyar zuwa Abuja,” in ji Atiku.
Jigon siyasar ya shirya ganawa da Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce rasuwar jigon ta taɓa zuciyarsa musamman idan ya tuna cewa ya shirya kawo masa ziyara idan ya ƙarasa Abuja.
Ya ƙara da cewa:
"Abin ya fi taɓa zuciyata saboda ya shirya zuwa ya kawo mani ziyara a har nan gidana.
"Buharin Dala ya kasance tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano sau biyu, kuma ya yi wa mutanensa hidima cikin kwarewa da gaskiya. Za a yi kewarsa matuƙa.”

Asali: Twitter
Atiku ya aiƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa
Atiku ya yi addu’ar Allah ya jikansa, ya gafarta masa, ya ba iyalansa da abokansa haƙurin jure wannan babban rashi da suka yi ba zato ba tsammani.
“Allah Ya saka masa da Aljannah Firdaus, ya gafarta masa, ya kuma ba iyalansa da dukan masoyansa juriya. Amin.”
Buharin Dala ya shahara a siyasar Kano, inda ya taba shugabancin ƙaramar hukumar Dala na tsawon zango biyu, kuma ya kasance ɗaya daga cikin jiga-jigan siyasa a yankinsa.
Tsohon Antoni-Janar ya rasu a Kwara
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Atoni-janar na farko a jihar Kwara, Alhaji Alarape Salman ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 81 a duniya.
Gwamnan AbdulRahman AbdulRazak ya yi alhinin wannan rashi tare da bayyana irin gudunmawar da marigayin ya bayar a lokacin da ya ke rike da mukamin kwamishinan Shari'a.
AbdulRazaq ya tura sakon jaje ga Sarkin Ilorin, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari da kuma Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) kan wannan.babban rashi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng