Masoyin Tinubu Ya Mika Bukatarsa ga Wike kan Dauda Kahutu Rarara

Masoyin Tinubu Ya Mika Bukatarsa ga Wike kan Dauda Kahutu Rarara

  • An buƙaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da ya karrama fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara
  • Wani masoyin Shugaba Bola Tinubu a jihar Bauchi, Khamis Musa Darazo ne ya yi wannan kiran ga ministan harkokin birnin Abuja
  • Khamis Musa Darazo ya bayyana cewa sanya sunan Dauda Rarara a wata hanya zai zama an yaba da irin gudunmawar da ya bayar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abuja - Wani masoyin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Khamis Musa Darazo, ya miƙa buƙatarsa ga Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan Dauda Kahutu Rarara.

Khamis Musa Darazo ya yi kira ga Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da ya sanya sunan Dauda Kahutu Rarara, a wani titi a Abuja domin girmama gudunmawar da ya bayar a fannin al’adu da siyasa.

An bukaci Wike ya sanya sunan Rarara a titi
Masoyin Tinubu ya bukaci Wike ya karrama Rarara Hoto: Khamis Musa Darazo, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Khamis Musa Darazo ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da jaridar Vanguard ranar Alhamis a Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masoyin Tinubu ya yabawa waƙoƙin Rarara

Masoyin na Shugaba Tinubu ya ce waƙoƙin Rarara sun zama hanyar haɗa kan ƴan Najeriya da kuma inganta zaman lafiya a tsakanin al’umma.

"Tun daga shekarar 1999, waƙoƙin Rarara suna taka rawar gani wajen tara magoya baya a lokacin yaƙin neman zaɓe, ƙarfafa haɗin kai na ƙasa, da kuma ba wa miliyoyin mutane ƙwarin gwiwa a sassan ƙasar nan."

- Khamis Musa Darazo

Sai dai Legit Hausa ba ta da tabbacin cewa Dauda Rarara ya yi wakokin siyasa a 1999 amma ya yi fice musamman gabanin zaben 2015.

Khamis Musa Darazo wanda ya riga ya aika da wasiƙa zuwa ga Nyesom Wike game da lamarin, ya bayyana Rarara a matsayin wanda ya fi ace masa mawaƙi ne kawai.

A cewarsa, kalaman waƙoƙin Rarara suna tasiri a cikin ƙabilu kuma sun taka muhimmiyar rawa a tsarin siyasar Najeriya.

“Waƙoƙin Rarara ba waƙa kawai ba ce. Cike suke da saƙonnin zaman lafiya, ci gaba, da juriya. Waƙoƙinsa sun zama kamar taken ƙasa a tarurruka da gangamin siyasa, suna inganta haɗin kai."

- Khamis Musa Darazo

Meyasa ake so Wike ya karrama Rarara?

Ya ƙara da cewa sanya sunan Rarara a sabon titi zai kasance wata hanya ta girmama gudunmawar da ya ba da.

Masoyin Tinubu ya bukaci a karrama Rarara
Masoyin Tinubu ya yaba da wakokin Rarara Hoto: Khamis Musa Darazo
Asali: Facebook

Ya nuna cewa hakan zai tabbatar da cewa matasa da masu tasowa za su san rawar da ya taka a tarihin al’adu na Najeriya.

"Ba wai kawai batun sakawa baiwar da yake da ita ba ne. Hanya ce ta nuna cewa fasaha tana da tasiri wajen gyara al’umma da kuma zaburar da ƙasa gaba ɗaya."

- Khamis Musa Darazo

Rarara ya fitar da sabuwar waƙa

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara ya fitar da wata sabuwar waƙa.

Dauda Kahutu Rarara ya caccaki shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Abdulrahman Tchiani da ya yi juyin mulki a 2023 .

Sakin waƙar dai na daga cikin alƙawarin da ya ɗauka ne na sakin waƙoƙin caccakar Tchiani har guda tara, domin adawa da mulkin da yake yi a Jamhuriyar Nijar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng